Tottenham ta kara yaga ɓarakar Everton a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta caskara Everton 4-0 a wasan mako na biyu a Premier League da suka fafata ranar Asabar.
Minti na 14 da fara wasa Tottenham ta ci ƙwallo ta hannun Yves Bissouma, sannan ƙyaftin Son Heung-Min ya kara na biyu a minti na 25 da kuma a minti na 77.
Tottenham ta zura na huɗu ne a raga ta hannun Cristian Romero, saura minti 19 a tashi daga wasan da ta haɗa maki ukun da take bukata.
Karo na biyu kenan da aka doke Everton a kakar bana, bayan da Brighton ta je ta ci 3-0 ranar Asabar 18 ga watan Agusta a Goodison Park.
Kaka biyu baya, Everton ta kasa cin wasannin da take buga wa a cikin watan Agusta a Premier League.
Ita kuwa Tottenham ta fara da tashi 1-1 a King Power da Leicester ranar Litinin a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.
Ranar Lahadi 1 ga watan Satumba, Tottenham za ta je gidan Neewcastle United a wasan mako na uku a Premier League.
Ita kuwa Everton za ta fafata da Doncaster ranar Talata a League Cup, sannan ta karɓi bakuncin Bournemouth a wasan mako na uku a Premier League ranar Asabar 31 ga watan Agusta.
Everton ta yi fama da ƙalubale a bara, wadda da ƙyar ta samu damar ci gaba da buga Premier League ta bana, bayan da aka kwashe mata maki.
Jerin ƴan wasan da Everton ta ɗauka a bana
- Tim Iroegbunam daga Aston Villa
- Jack Harrison daga Leeds United
- Omari Benjamin daga Arsenal
- Iliman Ndiaye daga Marseille
- Waɗanda ta ɗauka aro
- Jesper Lindstrom daga Napoli
- Jake O'Brien daga Lyon
- Asmir Begovic, wanda bai da ƙwantiragi










