Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mbappe ya sanar da PSG ba zai wuce 2024 a kungiyar ba
Kylian Mbappe ya ce ya sanar da Paris St-Germain a cikin watan Yulin 2022 cewar ba zai zauna a kungiyar fiye da karshen kakar 2024 ba.
Yarjejeniyar dan wasan mai shekara 24 za ta kare a karshen badi da cewar za a iya tsawaita masa shekara daya.
A baya ya aika wa kungiyar da wasikar cewar ba zai ci gaba da taka leda a kungiyar da zarar wa'adinsa ya cika a birnin Paris.
Kenan PSG za ta yi shirin sayar da Mbappe a kakar nan, idan ba haka ba za ta yi asararsa a matakin wanda yarjejeniyarsa ta kare a kungiyar.
Real Madrid ta dade tana bibiyar dan kwallon tawagar Faransa, wanda ya watsa mata kasa a ido da cewar ya zabi ci gaba da taka leda a PSG a bara.
Bayan da Karim Benzema ya koma taka leda a Saudi Arabia, hakan na nufin Real na neman mai cin kwallo da zai maye gurbinsa, koda yake ana alakanta Harry Kane na Tottenham da cewar shine za ta dauka.
Mbappe, ya fara yi wa PSG wasannin aro a 2017 daga Monaco, daga baya ta sayi dan wasan kan Yuro miliyan 180, wanda yanzu ya ci kwallo 212 a wasa 260.
Ya ci wa Faransa kwallo 38 a karawa 68 har da uku rigis da ya ci a wasan karshe a gasar kofin duniya a Qatar, inda suka yi rashin nasara a hannun Argentina a bugun fenariti.
Mbappe ya zama na daya a Ligue 1 a cin kwallaye karo biyar a gasar, wanda ya lashe kofin lik biyar daga kaka shida a PSG.
Ligue 1 kadai PSG ta dauka a 2022-23, hakan ya sa ta kasa daukar Champions League a bana, kofin da take son dauka, wadda Bayern Munich ta fitar da ita a zagayen 'yan 16.
Mbappe zai zama na biyu da ake biya albashi mai tsoka da zai bar PSG a bana, bayan Lionel Messi da zai koma buga gasar kwallon kafa ta Amurka a Inter Miami.
Ana kuma alakanta Neymar daya daga fitatcen dan kwallon PSG da cewar zai koma taka leda a Saudi Arabia a badi.