Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier
Arsenal ta doke Wolverhampton 2-1 a wasan mako na 14 a Premier League da suka kara ranar Asabar a Emirates.
Minti shida da fara wasa Arsenal ta ci kwallo ta hannun Bukayo Saka, sannan Martin Odegaard ya kara ni biyu a minti bakwai tsakani.
Daga baya ne Wolverhampton ta zare daya ta hannun Matheus Cunha, saura minti hudu lokaci ya ci.
Kwallon da Saka ya ci ya zama na 100 da Gunners ta zura a raga a dukkan fafatawa a 2023, ta zama ta biyar mai kwallo 100 ko sama da haka a manyan gasar Turai.
Ta farko ita ce Man City mai 137, sai Real Madrid mai 119 da Bayern Munich mai 111 da kuma Bayer Leverkusen mai 110 a raga.
Arsenal ta doke Wolverhampton karo na biyar a jere kenan, ta kuma ci wasa uku a jere a Premier League.
A kakar 2022/23 da Wolverhampton ta kai ziyara Emirates, Arsenal ta yi nasarara sharara 5-0 ne.
Da wannan sakamakon Gunners ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 33, bayan mako na 14.
Arsenal wadda ta kai zagaye na biyu a Champions League mai maki 12 a rukuni na biyu za ta je gidan PSV Eindhoven a cikin watan nan, karawar karshen rukuni.