Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin Gasar Kofin Duniya
Tarihin Just Fontaine na zura ƙwallo 13 a raga a gasar cin kofin duniya guda ɗaya da ya buga abin mamaki ne.
Ka yi la'akari da cewa ba takalmansa ya saka ba, kuma bai cancanci shiga cikin ƴan wasa 11 da suke buga wa Faransa tamaula ba.
Kuma bajintar da ya yi a lokacin ba a ba shi kyautar takalmin zinare ba a matakin wanda ya fi kowa yawan cin ƙwallaye a gasar 1958 - maimakon haka wata jaridar Sweden ce ta ba shi bindiga, saboda kasancewarsa "ƙwararre wajen iya buga ƙwallo ta faɗa raga".
Akan ambaci sunansa a duk bayan shekara huɗu kenan lokacin da ake buga gasar cin kofin duniya a matsayin ma'aunin auna fitattun ƴan wasan da ke buga gasar - Ko za a samu wanda zai ci ƙwallaye da yawa kamar nasa? amma har yanzu ba a kai ga bajintar da ya yi a gasa ɗaya ba.
A gasar cin kofin duniya ta 2026, wasu daga cikin fitattun masu zura ƙwallaye a raga suna matsowa kusa da tarihinsa fiye da yadda aka kalubalance shi a cikin shekaru masu yawa da suka gabata, yayin da Lionel Messi da Kylian Mbappe da Harry Kane da Jude Bellingham ke takara wajen neman lashe kyautar takalmin zinare da ake kira Golden Boot.
Tun daga 1970, sau uku kacal ne wanda ya fi kowa zura kwallaye a gasar cin kofin duniya ya samu fiye da kwallaye shida a gasa ɗaya. Mbappe da Messi sun sun ci ƙwallo takwas kowannensu, yayin da Erling Haaland yake da bakwai, Kane da Jude Bellingham kuma suna biye da shida-shida a raga a gasar 2026.
Yawan tawagogi da aka samu zuwa 48, ya sa an kara samun yawan buga wasanni da yawa, kuma yadda Argentina da Faransa da Ingila suka kai wasan daf da ƙarshe, dama ce ga Messi da Mbappe da Kane da kuma Bellingham ta kara cin ƙwallaye nan gaba daga baya a tantance gwaarzo a tsakaninsu a bana.
Amma duk da wannan fa'ida, har yanzu suna da tazarar ƙwallaye mai yawa tsakaninsu da mutumin da ya kafa tarihin a cikin wasanni shida da ya buga.
Idan aka kwatanta da waɗanda suka shafe shekara 68 da suka gabata suna ƙoƙarin karya tarihinsa ba tare da nasara ba, Fontaine ba sananne ba ne sosai ga masu kallon tamaula a wannan zamani.
Yayin da aka fi kallon Pele da Maradona da Messi da Ronaldo da sauran makamantansu a matsayin mafiya ƙwarewa a fannin taka leda, Fontaine ba abin yarwa ba ne kan irin bajintar da ya nuna a gasar kofin duniya kuma a karon farko da ya halarta.
Idan ka kalli rayuwa da sana'ar Fontaine a fannin taka leda mai ban mamaki ce - wanda, da a ce yana taka leda a zamanin yau, da watakila ya wakilci wata ƙasa dabam ba Faransa ba.
Wasan kwata fainal a gasar bana ta 2026 tsakanin Faransa da Morocco da aka buga, kowa ya san cewar karawar ta hamayya ce, kuma haka batun yake a wajen Fontaine. An haife shi a Marrakesh a watan Agustan 1933 - a lokacin, Morocco na ƙarƙashin mulkin Faransa ne.
Morocco ta samu ƴancin kai shekaru biyu kafin gasar cin kofin duniya ta 1958, amma a lokacin Fontaine ya riga ya zama fitaccen ɗan wasan mai taka leda a lig ɗin Faransa - saboda haka ne ya samu damar wakiltar Les Bleus, wato tawagar Faransa.
Kuma kamar yadda ɗan jarida mai labarin wasanni kuma masanin tarihi, Philip Barker ya bayyana wa BBC Sport, da abubuwa sun tafi yadda Faransa ta tsara tun farko, Fontaine ba zai buga wasa a gasar cin kofin duniya da aka yi a Sweden ba ma.
"Ba shi ne zaɓi na farko ba a zahiri - wani abokin wasansa [Rene Bliard] ya ji rauni a lokacin atisaye," in ji Barker. "An kuma yi canjin ne a mintin ƙarshe, har ma sai da ya aro takalma [daga abokin wasansa Stephane Bruey] domin wasan farko ne, kuma bai da wani takalmi da ya dace da shi."
Takalminsa ya lalace a wajen atisaye, kuma bai zo da madadinsu ba.
"Ka yi tunanin irin wannan yanayi a wannan zamanin, ya sha bamban sosai da abin da yake faruwa a yanzu," in ji Barker.
"An yi wa Fontaine tiyata a gwiwarsa a lokacin kakar wasan, kafin fara gasar kofin duniya, don haka akwai shakku kan ko zai iya buga gasar.
Amma hakan ya sa aka gayyace shi zuwa gasar, sannan ya je da ƙoshin lafiya - wasu ƴan ƙwallon da yawa sun buga wasannin da suka sha musu kai ga kuma ɗan karen gajiya kafin fara gasar cin kofin duniya''.
Fontaine ya buga wa Faransa wasa biyar a lokacin da koci Albert Batteux ya saka shi cikin jerin ƴan wasa 11 na farko, amma ba baƙo ba ne a duniyar a fannin ƙwallon ƙafa.
Da yake magana da BBC a watan Afrilun 2002, Fontaine ya ce bai taɓa tunanin kafa tarihin wanda zai fi kowa zura kwallaye ba a gasar kofin duniya.
"A wancan lokacin ba mu fuskantar matsin lamba sosai," in ji Fontaine. "'Yan jarida biyu ne kawai ke bin tawagarmu.
"Shugabanninmu sun yi imanin cewa za a fitar da mu daga gasar da wuri, har ma suka ba mu riguna uku kacal kowannenmu, saboda haka ba mu da wani matsin lamba ko fuskantar ƙalubale ko kaɗan.
"Hankalina bai kai ga kafa tarihin yawan zura kwallaye ba a raga sam. Har ma na ƙi buga fenariti a wasan neman matsayi na uku!"
Ya buga wa Reims tamaula, ƙungiyar da ta lashe gasar lig da kofin Faransa a kakar 1957-58. Wannan na ɗaya daga cikin kofunan Ligue 1 guda huɗu da Fontaine ya lashe - ɗaya tare da tsohuwar kungiyarsa Nice, uku kuma tare da Reims.
Shekara guda bayan gasar cin kofin duniya, Fontaine ya taimaka wa Reims kai wa wasan ƙarshe a European Cup - inda suka sha kashi a hannun Real Madrid - bayan da ya zama wanda ya fi kowa zura kwallaye a gasar ta zakarun Turai a1958-59 da kwallaye 10.
Kuma abokan wasansa suna girmama shi sosai, ciki har da Raymond Kopa - tauraron tawagar Faransa wanda daga baya ya lashe Ballon d'Or a 1958, yayin da Fontaine ya zo na uku.
Fontaine ya ci ƙwallo uku a gagarumar nasarar 7-3 da Faransa ta samu a kan Paraguay a wasan farko a Rukuni na Biyu, kuma hakan ne ya sa ya fara shiga kan gaba a nasarorinsa.
Haka kuma ya ci ƙwallo a kowane wasa, ciki har da zagayen kusa da na ƙarshe, lokacin da Brazil mai tawaga mai ƙarfin gaske wadda take da Pele mai shekara 17 ta doke Faransa da ci 5-2.
Wasan neman matsayi na uku ya ba Fontaine dama, duk da takalmin aro yake amfani da shi - kuma ya yi amfani da damar da ya samu, inda ya ci ƙwallaye huɗu a lokacin da Faransa ta yi gagarumar nasarar 6-3 a kan Jamus ta Yamma.
Abin da ya fi ɗaukar hankali game da waɗannan ƙwallaye da ya zura a raga ba yawansu kaɗai ba ne, har ma da ingancinsu.
Fontaine ba wani ɗan wasa ne da yake amfani da ƙarfi kawai a zamanin talabijin baki da fari ba, lokacin da ake buga ƙwallon da aka yi da fata ga nauyi, kuma masu tsaron raga ba su da cikakkiyar kariya daga hare-haren ƴan wasa masu kai hari.
Idan aka kalli lokacin da ya yi bajinta daga shekarar 1958, Fontaine yana kama da ɗan wasan da zai yi fice a ƙwallon ƙafar wannan zamani.
A wasan da Paraguay, ya kutsa cikin masu tsaron baya ya kuma karya tarkon satar gida, sannan ya ci ƙwallo mai ƙyau ta kusurwa.
"Fontaine yana kama da ɗan wasan gaba na zamanin nan, yana da matuƙar sauri," in ji Barker. "Jaridar L'Equipe ta ce ya kasance mai jagorantar kai hari irin na salon Ingilishi - mai jarumtaka, mai fafutuka, mai sa kaimi babu tsoro
"Sannan idan ka ci ƙwallo uku rigis a wasan farko a gasar, dole ne hakan ya ba ka kwarin gwiwa sosai."
Ƙwallo uku rigis da ya ci Jamusawa sun yi ƙyau kuma na musamman - ya karɓi ƙwallo a tsakiyar fili, sai ya tserewa masu tsaron baya, sannan ya ci ƙwallo ta kusurwar raga, salon irin ƙwallon da Michael Owen ya ci wa Ingila a kan Argentina a shekarar 1998.
Yawan kwallayen da Fontaine ya ci ya dace da yanayin gasar cin kofin duniya ta 1958, inda aka zura 126 a raga - adadi na biyu mafi yawa a tarihin gasar da tawaga 16 suka halarta, bayan ta 1954. Faransa ce kasar da ta fi kowa zura kwallaye, inda ta ci 23.
Da ƴan wasa irin su Fontaine da Kopa, Barker na ganin cewa tawagar Faransa ta 1958 za a iya kwatanta ta da mafi kyau - fiye da ta zamanin nan.
"Gasar 1958 ita ce gasar cin kofin duniya ta ƙarshe da aka ga an ci yawan kwallaye a raga sosai. Akwai tawagar Brazil mai tasowa tare da Pele, amma Faransa ma tana cikin mafi girma a tarihi," in ji shi.
"Muna yawan magana game da tawagogin 1998 da 2018, amma wannan ita ce tawagar Faransa ta farko mai girma. Ƴan wasa biyar na gaba sun ci ƙwallaye 22, kuma hakan ya nuna irin ƙarfin da suke da shi.
"Eh, masu tsaron baya suna da ɗan nauyi a lokacin, amma yadda Faransa ke taka leda, sun iya ci kowace tawaga ƙwallaye. Fontaine ma yana taimaka wa Kopa ya ci ƙwallaye, tawaga ce mai matuƙar haɗin kai.
"Brazil ta 1958 ce kawai ta dakatar da Faransa, ɗaya daga cikin mafiya girman tawagogi a tarihin ƙwallon ƙafa.
Duk da cewa ana girmama Fontaine a matsayin wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a gasar cin kofin duniya ta 1958, bai taɓa samun ƙyautar Golden Boot ba - domin ba a fara bayar da ƙyautar ba sai a 1982.
A shekara ta 2014, Fifa ta ba shi takalmin platinum na musamman domin karrama bajintarsa da har yanzu ba a samu wanda ya yi ƙwazonsa ba a yawan cin ƙwallaye.
"Babu kyautar Golden Boot ko wani abu makamancin haka a 1958, saboda haka babu wanda ya damu da ita," in ji Fontaine. ".
"A yau, da zarar ɗan wasan gaba ya ci ƙwallaye uku, kowa sai ya fara tambayarsa game da tarihin.
Tun daga lokacin, Gerd Muller ne kaɗai ya ci ƙwallaye 10 a gasar cin kofin duniya a shekarar 1970 - kuma har yanzu ya gaza da ƙwallaye uku wajen kaiwa adadin na Fontaine.
To me ya sa ba a ɗauki Fontaine a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa mafiya girma a tarihi ba?
Amsar ita ce rauni.
A watan Maris na 1960, Fontaine ya karya ƙafa yayin wani wasan lig a Faransa. Raunin ya ƙara tsananta a yayin ƙoƙarinsa na dawowa taka leda sau da dama, kafin daga ƙarshe a tilasta masa yin ritaya daga ƙwallon ƙafa a 1962.
A lokacin yana da shekara 28 kacal.
Kididdigarsa ta ƙarshe a matakin babban ɗan wasa wasan ƙasa da ƙasa daga wasa 21 da ya buga wa Faransa, ya ci ƙwallo 30.
Sakamakon haka, Fontaine bai sake komawa fagen gasar cin kofin duniya ba. Mutum zai iya tunanin irin nasarorin da Faransa za ta iya samu da a ce ya halarci gasar da aka yi a 1962 ko ta 1966.
Bayan da ya yi ritaya daga taka leda, Fontaine ya ci gaba da kasancewa a harkar ƙwallon ƙafa. Ya taimaka wajen kafa ƙungiyar ƴan wasan Faransa, UNFP, inda ya zama shugabanta na farko a 1961.
Ya kuma yi aikin horarwa na wani lokaci, ciki har da jagorantar tawagar Faransa a wasanni biyu a 1967. Daga baya ya horar da PSG da Toulouse, kafin ya shafe shekaru biyu tare da Morocco - ƙasar da aka haife shi.
"Ya kafa ƙungiya, ya yi horarwa, ya gudanar da shagunan sayar da kayan wasanni guda biyu. Daga lokaci zuwa lokaci, mutane kan tambayi wanda ke riƙe da tarihin zura kwallaye a gasar cin kofin duniya, kuma har yanzu yana jin daɗin cewa mutane suna tuna shi," in ji Barker.
"Fontaine ya kan yi barkwanci cewa idan ya dawo bayan shekaru 200, tarihinsa zai ci gaba da kasancewa. L'Equipe ta kira shi 'wanda ba za a iya karya tarihinsa ba'."
Fontaine ya rasu a ranar 1 ga Maris 2023 yana da shekara 89. Ya kuma ga lokacin da Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyu, sannan ya ga fitowar fitaccen ɗan wasan gaba na yanzu, Mbappe - ɗaya daga cikin mutanen da za su iya karya tarihin nasa.
"Yaya dacewa za ta kasance idan Mbappe ya karya tarihinsa?" in ji Barker.
"Amma cin ƙwallo 13 adadi ne mai girma ne ƙwarai. Fontaine gwarzo ne na hakika wanda ba a cika yaba masa yadda ya kamata ba."