Wike ko Turaki: Wane tsagi INEC ta karɓi sunayen ƴantakararsa?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wani sabon rikici ya sake kunno kai a jam'iyyar PDP, bayan da ɓangaren Wike ya ce hukumar zaɓen Najeriya INEC, ta karɓi sunayen waɗanda za su yi wa jam'iyyar takara a zaben 2027 .

Wannan matakin dai ya haifar da musayar kalamai tsakanin ɓangaren Wike da Tanimu Turaki, da ke da'awar su ne halattatun shugabannin jam'iyyar bayan wani hukunci da wata babbar kotun ƙasar ta yanke.

Wike dai ya tabbatar da cewa hukumar zaɓen ƙasar ta ba su lambobin shiga shafinta domin wallafa sunayen waɗanda za su yi wa PDP takara.

To sai dai ɓangaren Tanimu Kabiru Turaki, ya ce ba za ta saɓu ba.

Yanzu haka dai ɓangarorin biyu na gaban kotun ƙoli domin sauraren hukuncin ƙarshe da zai tabbatar da makomar jam'iyyar.

Mene ne martanin tsagin Tanimu Turaki?

Ɓangaren Turaki na ganin ikiririn na Wike abu da mai kama da almara, domin kuwa matakin ya bayar da mamaki a cewar tsagin.

Farida Umar ita ce mai magana da yawun ɓangaren Tanimu Turaki, ta shaida wa BBC cewa, su ma sun riga sun kai dukkan abubuwan da INEC ke buƙata akan ƴantakarara, don haka idan har an karɓi na ɓangaren Wike, to suna ɓata lokacinsu ne.

"Magana na gaban kotu yanzu haka, umarnin da kotun ƙoli ta bayar shi ne kwamitin amintattu ne ke da ikon naɗa shugaban jam'iyya a PDP, kuma kwamitin ya naɗa shugabannin riƙo, don haka su ne za su kai sunayen ƴantakarar PDP, ba ɓangaren Wike ba."

Ai mu ne masu jam'iyya - Tsagin Wike

Su ma a nasu ɓangaren na Wike, sun ce abokan jayayyarsa na ɓata lokacinsu wajen yaudarar ƴantakarar da suke mara wa baya ta hanyar karɓar kuɗaɗensu na sayen fom alhali ba su ne hukumar ta INEC ta amince da su ba.

Muhammed Jangudu Haruna shi ne mai magana da yawun ɓangaren na Wike, ya shaida wa BBC cewa duk da cewa magana tana kotu, amma ba kan rikici da shugabancin jam'iyyar ba.

''Muna kotu ne dangane da ƙarar da muka kai INEC kan muna so ta amince da shugabancinmu, amma ba da tsaginsu Turaki ba'', in ji shi.

Ya yi iƙirarin cewa batun Turaki, ai INEC ma ba ta san da zamansa ba.

Me INEC ta ce?

Kawo yanzu dai hukumar zaɓen ƙasar, INEC ba ta tabbatar da iƙirarin ɓangaren na Wike ba, kodayake ba ta musanta ba.

Cikin wata hira da BBC ɗaya daga cikin masu magana da yawun hukumar, Hajiya Zainab Aminu ta ce rikicin jam'iyya bai shafi INEC ba.

''Ai rikicin jam'iyya abu ne na cikin gida tsakanin mambobin jam'iyya, bai shafi hukumarmu ta INEC ba'', kamar yadda ta bayyana.

Wannan dambarwa dai na zuwa ne a daidai lokacin da INEC ta ƙara wa'adin lokacin da jam'iyyu za su miƙa sunayen ƴan takararsu har ya zuwa ranar 14 ga wannan watan na Yuli na 2026.