Gasar Kofin Duniya 2026: Hanya uku ta tantance wanda zai lashe takalmin zinare

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Yayin da Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA 2026 ke ƙara shiga matakin ƙarshe, fafatawar neman kyautar takalmin zinare ta zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka mamaye hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.

Duk da yake ƙasashe na fafatawa ne da burin ɗaga kofin duniya, fitattun ƴan wasa kuwa na kokarin ganin cewar sun yi suna sun kuma yi fice wajen yawan zura ƙwallo a raga a babbar gasar tamaula ta duniya da ake yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Tuni dai aka kai matakin daf da karshe, inda za a kara tsakanin Faransa da Sifaniya da kuma kece rainin tsakanin Ingila da Argentina mai rike da kofin da ta lashe a 2022 a Qatar kuma na uku jimilla.

A halin yanzu, Kylian Mbappé na Faransa da Lionel Messi na Argentina ne ke jagorantar jerin waɗanda ke kan gaba a zura ƙwallaye a raga masu takwas kowanne.

Sai dai Mbappé ne ke riƙe da matsayi na farko saboda ya fi Messi yawan bayar da ƙwallayen da aka zura a raga, bayan takwas da ya ci, wanda shi ne ma'aunin da ake amfani da shi wajen raba gardama idan ƴan wasa sun ci yawan ƙwallaye iri ɗaya.

Masu biye da su kuwa akwai Erling Haaland na Norway mai ƙwallaye bakwai, sai dai an yi waje da kasarsa daga wasannin bana a hannun Ingila a zagayen kwata-fainal.

Sauran da suke takara sun haɗa da Harry Kane da Jude Bellingham daga Ingila da kowanne yake da shida.

  • Kylian Mbappé (Faransa) – ƙwallaye 8
  • Lionel Messi (Argentina) – ƙwallaye 8
  • Erling Haaland (Norway) – ƙwallaye 7
  • Harry Kane (Ingila) – ƙwallaye 6
  • Jude Bellingham (Ingila) – ƙwallaye 6

Sai dai duk da yadda aka samu ƴan wasa da yawa da ke takarar lashe takalmin zinare a bana, masana na ganin cewa akwai muhimman abubuwa uku da za su tantance wanda zai fi kowa zura ƙwallo a ƙarshe.

Abin da ya sa Mbappé da Messi suka fi sauran ƴan wasa damar lashe takalmin zinare ba wai yawan ƙwallaye kaɗai da suka ci ba ne. Ƙasashensu sun kai matakin gaba a gasar, wanda ke ba su ƙarin wasanni da damar ƙara yawan cin ƙwallaye a raga.

A gefe guda, Haaland na fuskantar matsala saboda Norway ta riga ta fita daga gasar, don haka ƙwallayensa sun tsaya a inda suke wato bakwai, kuma tuni Mbappe da Messi suna gabansa, kenan ya fice daga cikin masu takara.

Wannan shi ne ainihin dalilin da ya sa masana ke amfani da hanyoyi uku: yawan ƙwallayen da ɗan wasa ya ci, yawan wasannin da suka rage wa kasar, da kuma irin yanayin wasan da ɗan ƙwallon ke bugawa a halin yanzu.

Idan aka kalli waɗannan abubuwa gaba ɗaya, Mbappé da Messi ne suka fi kowa samun damar lashe kyautar takalmin zinare, yayin da Kane da Bellingham ke jiran wata dama ta musamman domin tarar da su a yawan zura ƙwallaye a raga a gasar bana.

Bari mu duba dalili uku da za a bi a tantance wanda zai iya lashe takalmin zinare a gasar cin kofi duniya ta 2026.

Yawan ƙwallayen da ɗan wasa ya zura a raga

A al'adar ƙwallon ƙafa, ana cewa "wanda ya fara cin kasuwa shi ne mai yin ciniki da yawa." Wannan karin magana ta dace da takarar kyautar takalmin zinare a gasar kofin duniyar nan.

Ɗan wasan da yake kan gaba wajen cin ƙwallaye yana da fa'idar da sauran masu bibiyarsa ba su da ita.

Mbappé da Messi sun riga sun bayar da tazarar ƙwallaye a kan abokan hamayyarsu. Duk wani ƙwallo da ɗaya daga cikinsu zai sake ci a mataki na gaba ka iya zama matakin da zai raba shi da sauran masu takara. Wannan ne ya sa kowace damar da suke samu a wasan gaba ke zama mafi mahimmaci a wannan fannin.

Duk da haka, tarihin Kofin Duniya ya nuna cewa fara cin ƙwallaye da yawa da zarar an fara gasar a wani lokaci ba shi ne tabbacin lashe takalmin zinare ba. Sau da dama an ga wasu ƴan wasan sai daga baya suke samun damar zura ƙwallaye da yawa a raga su kafa tarihin bajinta a zagayen ƙarshe.

Wannan yana nufin cewa Kane ko Bellingham na da damar sauya salon gasar idan suka samu damar zura ƙwallaye a wasannin da suka rage.

Domin suna matakin daf da karshe, suna da damar buga wasan neman mataki na uku idan suka yi rashin nasara, idan suka doke Argentina su kai zagayen karshe, kenan suna wasa biyu nan gaba ko mai zai faru kodai neman mataki na uku ko na lashe kofin duniya.

Yawan wasannin da suka rage

Wata muhimmiyar hanya da ke taimakawa wajen hasashen wanda zai lashe takalmin zinare ita ce nazarin yawan wasannin da ɗan ƙwallon zai iya bugawa kafin ƙarshen gasar.

A nan ne Mbappé da Messi suka sake samun wata babbar damar. Faransa da Argentina suna ci gaba da taka rawar gani a gasar, waɗanda ke da fitattun ƴan wasan da suke da damar samun ƙarin mintuna da ƙarin yawan wasanni domin ƙara yawan cin ƙwallaye nan gaba.

A gefe guda kuma, Haaland duk da cewa yana da ƙwallaye bakwai, damar sa ta ragu sosai bayan ficewar Norway daga gasar. Idan ɗan wasa ya fita daga gasar, adadin ƙwallayensa na nan yadda yake ba tare da wata damar ƙara su a raga ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa wasu lokuta ɗan wasan da yake matsayi na uku ko na huɗu kan iya komawa baya idan waɗanda suke gaba sun ci gaba da buga wasanni.

Ingila kuwa tana da ƴan wasa biyu a cikin biyar na farko a cin ƙwallaye a bana. Kane da Bellingham suna da ƙwallaye shida kowannensu, kuma idan suka ci gaba da samun damar cin ƙwallaye a raga, za su iya matsawa kusa da Mbappé da Messi. Wannan na nuna cewa har yanzu batun wanda zai lashe takalmin zinare a gasar cin kofin duniya tana buɗe.

Yanayin wasa da tasirin ɗan ƙwallo

A ƙwallon ƙafa, ba a lashe manyan kyautuka da suna ne kawai ba. Ana yin nasara ne idan aka yi aiki tukuru da juriya a filin wasa. Wannan ya sa masana ke ba da muhimmanci ga yanayin ƙwazon ɗan ƙwallo a lokacin gasar.

Mbappé ya nuna bajintarsa tun daga farkon gasar. Saurinsa, iya cin ƙwallaye da kuma yadda yake samun sarari a gaban masu tsaron baya, sun sa ya kasance barazana ga kowace tawaga da ta fuskance shi. Haka kuma, kasancewarsa mai bayar da ƙwallo a zura a raga ya kara ba shi ƙarin maki a ma'aunin FIFA idan yawan ƙwallayen da ya ci suka yi iri ɗaya da na Messi - Ɗan kasar Faransa ne za a bai wa ƙyautar bana.

Messi kuwa ya sake tabbatar da cewa shekaru ba su hana shi sa hazaka da ta kai yana haskakawa ba. Duk da cewar yana cikin shekaru 39 da haihuwa, ya ci gaba da zama tauraron Argentina ta hanyar zura ƙwallaye masu muhimmanci da kuma jagorantar kasar a manyan lokuta.

Kasancewar ya zura ƙwallo takwas a raga a wasannin bana, ya nuna cewa har yanzu yana taka rawar gani da nuna ƙwazo da bajinta, ba abin yarwa bane.

A bangaren Ingila kuma, Kane da Bellingham suna nuna ƙwazo sosai da ake da babban buri a kan ƴan wasa biyu. Kuma wani abin ban sha'awa duk lokacin da Kane ya kasa taka rawar gani sai Bellingham ya nuna kansa, haka kuma duk ranar da Bellingham ya kasa cin ƙwallo, sai Kane ya shige gaba a matakinsa na ƙyaftin.

Kane na amfani da gogewarsa wajen cin moriyar duk damar da aka samu, yayin da Bellingham yake nuna irin ƙarfin da ba kasafai ake gani daga ɗan wasan da ke buga gurbin tsakiya ba. Wannan haɗin gwiwa na iya zama makamin da zai taimaka wa Ingila wajen ci gaba da yin abin kirki a gasar da kuma ba ɗaya daga cikinsu damar shiga sahun gaba wajen neman ƙyautar takalmin zinare.

Duk wanda ya kalli jerin waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye a gasar cin kofin duniya a 2026, zai fahimci cewa takara tsakanin ƴan wasan ta yi tsauri fiye da yadda aka zata tun farko.

Mbappé da Messi ne ke kan gaba da ƙwallaye takwas kowanne, amma Kane da Bellingham na ci gaba da taka rawa da ƙalubalantarsu, yayin da Haaland ya kwan da sanin adadin da ya zura a raga ba za su bashi damar ci gaba da takara ba, sai dai ya jira gasar 2030.

Idan za a yi hasashen wanda zai iya lashe takalmin zinare a gasar bana, akwai abubuwa uku da za a kalla: yawan ƙwallayen da aka riga aka ci, yawan wasannin da suka rage wa kasar da kuma ɗan wasa, da kuma ƙwazon ɗan ƙwallon a filin daga.

A wannan lokaci, waɗannan ma'aunai na nuna cewa Mbappé da Messi ne suka fi kusa da samun nasara, amma kamar yadda Hausawa ke cewa, ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.