Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shekara ɗaya bayan rasuwar Buhari: Me ƴan Najeriya ke cewa?
Shekara ɗaya bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, abokan tafiyarsa a lokacin da yake raye sun shirya wani gagarumin taron tunawa da shi a Abuja babban birnin ƙasar.
Buhari na daga cikin ƴan siyasa ƙalilan waɗanda suke da tarin mabiya da masoya a lokacin rayuwarsa, lamarin da ya sanya ya riƙa samun ɗimbin ƙuri'u a duk lokacin da ya yi takara, tun yana faɗuwa, har zuwa lokacin da ya samu nasarar zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.
A ranar 13 ga watan Yulin 2025 ne tsohon shugaban ƙasar ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan, shekara biyu bayan sauka daga mulki.
A taron da aka shirya na tunawa da rasuwar tasa a Abuja, babban birnin Najeriya iyalai da abokai sun taru inda suka riƙa faɗin abubuwan da suka sani game marigayin.
BBC ta tattauna da wasu daga cikin mahalarta taron.
Abin da ya faru lokacin da na je wurin Buhari a Landan - Kashim
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima wanda ya gabatar da jawabi a lokacin taron ya tuno da abubuwan da suka faru jim kaɗan gabanin rasuwar tsohon shugaban ƙasar.
Ya ce shugaban Najeriya Bola Tbu ne ya umarce shi ya je birnin Landan inda Muhammadu Buhari ke jinya, kuma ya tabbatar cewa an yi duk abin da ya kamata.
Ya ƙara da cewa "Lokacin da na je sai likitansa ya shiga da ni inda yake (Buhari), sai na iske yana bacci, sai likitan ya ce zai tayar da shi, amma na ce 'ka bar shi'.
"Sai na fito da hawaye a idanuna, nan ne na iske Zahra da Yusuf a baƙin ƙofa, lokaci ne mai taɓa zuciya.
"Sannan karrama ni da aka yi wajen wakiltar shugaban ƙasa a matsayin wanda ya raka gawarsa gida, wannan na daga cikin babbar karramawar da shugaban ƙasa da kuma iyalin marigayi Muhammadu Buhari suka yi min".
'Yanzu aka fi buƙatar Buhari'
Ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Kano Alhassan Ado Doguwa ya tuna baya, tare da kwatanta halin da Najeriya ke ciki a yanzu da kuma wasu abubuwan da suka faru a lokacin mulkin tsohon shugaban.
Ya ce "Buhari ya zama abin alfahari ga mutanen Najeriya da mutanen Arewa.
"Za ka iya kwatanta Buhari da su irin su Sir Ahmadu Bello da irin su Abubakar Tafawa Balewa wajen yi wa ƙasa hidima, waɗanda ba su so kansu ba, ba su tara wa kansu abin duniya ba.
"Mutum ne wanda za a iya cewa an yi asararsa a daidai wannan lokacin da ƙasar ta shiga wani yanayi da irin su ake nema su ba da irin gudumawar da ƙila da an samu sauƙin abubuwan da ke fuskantar ƙasar nan," in ji Doguwa.
'Komai na tuna min da mahaifinmu'
Ita kuwa ƴar marigayin, wato Zahra Buhari ta bayyana cewa har yanzu mahaifina nasu na nan kusa-kusa a cikin zukatansu.
"Kusan komai ma (na tuna min da babanmu), domin ya kasance a kullum kana so ka bi yadda yake yin abubuwan shi.
"Idan abu mai muhimmanci ya faru sai ka ji in da daddy na nan me zai yi ko me zai ce?"
'Nakan ba shi shawara daga ni sai shi'
Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, wanda ke cikin mutanen da suka halarci taron ya ce Muhammadu Buhari ya ba shi dama a lokacin da yake raye domin ya riƙa ba shi shawarwari kan muhimman abubuwa.
"Ina daga cikin wadandada ya ba ni wata dama, ya ce min duk lokacin da na hangi wata shawara wadda za ta zama alkhairi ga amanar da yake ɗauke da ita yana so na sanar da shi.
"Gwargwadon iko nakan ba shi shawara a duk lokacin da na ga wani abu na gyara ko wani abu da ya kamata, sau da yawa nakan zauna daga ni sai shi sai Allah."
Abin da Buhari ya riƙa faɗa min - Zangon Daura
Ɗya daga cikin aminan marigayin, Sani Zangon Daura ya ce Buhari kan yi duk wani aiki da zuciya ɗaya.
"Komai zai yi zai tsaya ya yi da zuciya ɗaya, yana son ganin kowa ya yi gaskiya gwargwadon hali.
"Muna tare da shi tun yana samari, kullum abin da yake ce min shi ne 'ba zan yi abin da zai ɓata mini fansho dina ba', wato shi a kullum yana son ya gama da aikinsa lafiya kuma ba ya cikin duk wani abu da ya shafi maguɗi ko karɓar kuɗin mutane," in ji Sani Zangon Daura.
Me sauran ƴan Najeriya ke cewa?
BBC ta wallafa hoton marigayin a safiyar Litinin tare da tambayar abin da mutane za su fi tunawa da shi bayan shekara ɗaya da rasuwarwasa.
Muhammad Sani Hassan ya ce: Duk da bai cika goma ba amma ya fi Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon mai bai wa shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Akin Osuntokun ya ce duk da cewa Muhammadu Buhari ya rasu a matsayin "jarumi ga al'ummar arewacin ƙasar, amma bai yi mulki da kyau ba musamman wajen inganta rayuwar a'umma".