Arsenal ta fitar da Real ta kai daf da karshe a Champion League

Asalin hoton, EPA
Arsenal ta yi waje da Real Madrid a Champions League ta kai zagayen daf da karshe ranar Laraba a Santiago Bernabeu da cin 5-1 gida da waje.
Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Arsenal da cin 2-1 a wasa na biyu a kwata fainal a gasar ta zakarun Turai.
A makon jiya Arsenal ta doke Real Madrid 3-0 a Emirates a wasan farko zagayen kwata fainal a gasar ta zakarun Turai.
Arsenal ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Bukaya Saka, bayan da suka koma zagaye na biyu, tun farko Saka ya kasa cin fenariti a zagayen farko.
Daga baya ne Real Madrid ta farke ta hannun Vinicius Junior, bayan da Saliba ya yi sakaci aka ƙwace ƙwalin daga wajensa aka zura a raga.
Daf da za a tashi ne Arsenal ta kara na biyu ta hannun Gabriel Martinelli, kenan Gunners ta doke Real Madrid gida da waje a bana.
Wannan shi ne karo na biyu da Arsenal ta kai daf da karshe a Champions League, bayan 2009, kuma ba ta taɓa lashe kofin ba.
Real Madrid mai Champions League na bara mai 15 jimilla ta lashe shida daga ciki tun daga 2009.
Da wannan sakamakon Gunners za ta kara da Paris St Germain gida da waje zagayen daf da karshe a Champions League.
Sai dai PSG ta ci Manchester City a rukuni ta fitar da Liverpool a zagaye na biyu da yin waje da Aston Villa a kwata fainal.
Wasa tsakanin Real da Arsenal a Champions League:
Kakar 2024/2025
Champions League ranar Laraba 16 ga watan Afirilun 2025
- Real Madrid 1 - 2 Arsenal
Champions League ranar Talata 8 ga watan Afirilun 2025
- Arsenal 3 - 0 Real Madrid
Kakar 2005/2006
Champions League ranar Laraba 8 ga watan Maris 2006
- Arsenal 0 - 0 Real Madrid
Champions League ranar Talata 21 ga watan Fabrairun 2006
- Real Madrid 0 - 1 Arsenal
Ƴan wasan Real Madrid da suka kara da Arsenal
Masu tsare raga: Courtois, Fran González, Sergio Mestre.
Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger, Asencio.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim.










