Da gaske ne Boko Haram na amfani da jirgi maras matuƙi wajen kai hare-hare?

DRONE BAN IN NIGERIA

Asalin hoton, PA

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Rundunar sojin Najeriya mai yaki da kungiyar Boko Haram a shiyar arewa maso gabashin Najeriya, ta sanar da hana amfani da jirage marasa matuka da ka fi sani da 'Drones' a yankin.

Rundunar sojin ta ce duk da cewa akwai wannan doka da ta hana amfani da jiragen, amma jama'a da dama na ci gaba da amfani da su ba tare da izini a hukumance ba, inda kuma suke zargin ana amfani da jiragen marasa matuka wajen leken asirin hukumomin tsaro da sauran kayan gwamnati.

Rundunar sojin Najeriyar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai da ke yaki da mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP shiyar ta arewa maso gabas, Air Component Commander, Air Commodore U.U. Idris ya fitar.

Masana lamurran tsaro a Najeriya sun ce tabbas masu iƙirarin jihadi kan yi amfani da jirage maras matuƙi wajen kai wa sojoji hare-hare a Najeriya.

Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin samar da tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited, ya ce ko a watan Disamban 2024, mayaƙan sun kai wa sojoji hare-hare har sau hudu ta hanyar sanya bama-bamai jikin jiragen marasa matuƙi.

Dakta Kabir Adamu ya bayyana cewa ba yanzu waɗannan ƙungiyoyi suka fara amafani da jirgi maras matuƙi ba, "A 2019 mun ga lokuta inda waɗannan ƙungiyoyi suke amfani da jirage maras matuƙa amma kawai domin leƙen asiri, suna dasa bama-bamai a waɗannan jirage."

Rundunar sojojin Najeriyar a shiyar arewa maso gabas ta bayyana amfani da wadannan jiragen a matsayin wuce-gona da iri wanda ke da matukar barazana a ɓangaren samar da tsaro.

Kafin daukar wannan matakin hana amfani da wadannan kuramen jirage marasa matuka, akwai kamfanoni da dama da masu binciken kimiyya da 'yan safiyo da ma 'yan jarida da ke amfani da su.

Dakta Kabiru Adamu ya bayyana cewa akwai matakan da aka dauka da suka dace da su "Dole ne mutum ya cika sharuddan da doka ta tanada kafin ya yi amfani da irin waɗannan jirage."

Masanin lamurran tsaron ya kara da cewa muddin aka yi amfani da wannan doka sannan ta samu ɗorewa, akwai yuwar samun sauƙi a ɓangaren matsalolin tsaro da ke addabar yankin na arewa maso gabas da ma sauran sassan Najeriya.

A baya-bayan nan an samu ƙaruwar hare-hare daga ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, musamman a jihar Borno, wadda ita ce cibiyar rikicin.

Boko Haram ta kwashe kimanin shekara 15 tana kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a yankin Tafkin Chadi.

Kimanin mutum 36,000 ne aka yi ƙiyasin cewa ƙungiyar ta kashe, sannan ta tarwatsa sama da mutum miliyan biyu daga muhallansu.

Wannan lamari ya jefa al'umma da dama a yankin cikin halin ƙunci da yunwa da rashin tabbas.

Gwamnatin Najeriya ta ayyana cewa ta ci galaba a kan ƙungiyar, sai dai har yanzu mayaƙan na kai hare-hare lokaci zuwa lokaci.