Manchester United ta ci wasa na uku a jere a Premier

Ba a ci Manchester United ba a wasa 119 da ta buga a Premier matukar ta yi nasara a minti 45 din farko, rabon da a yi mata haka tun wanda Leicester City ta yi mata a 2014

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta ci wasa na uku a jere a Premier karkashin sabon mai horas da kungiyar Erik Ten Hag.

Wannan nasara ta kara jefa Leicester City cikin hadari, domin kuwa ta kara tabbatar da ita a matsayin ta karshe a teburin Premier.

A minti na 23 da fara wasan Marcus Rashford ya bai wa Jadon Sancho wata kwallo mai kyau ya jefa a raga, bayan ya yanka mai tsaron ragar Leicester.

Nasarar wata dama ce ta karfafawa Unietd gwiwa ta ci gaba da dorawa kan nasarar da ta samu a Liverpool da Southampton.

Duk da cewa ta yi nasara a zagayen farko na wasan, Leicester City ce ta samu damar rike zagaye na biyu.

Babu shakka wasan bai yi wa kocin kungiyar Brendan Rodgers dadi ba da duka wani magoyin bayan kungiyar, wadanda suke fatan ganin sun ci wasan farko a wannan kakar.

Golan United David de Gea ya yi kokarin cire wata kollo da aka James Maddison ya buga masa, a wani bugun tazara da suka samu.

Da wannan nasara United ta koma ta biyar a teburin gasar tana biye wa Brighton da ke matsayi na hudu baya, wadda ita kuma take biye wa Tottenham da ke matsayi na uku.

Manchester City ce ke matsayi na biyu, yayin da Arsenal ke matsayi na daya, wadda za ta barje gumi da United a ranar Lahadi mai zuwa.