Jack Grealish yana ƙamfar cin ƙwallaye a bana

Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Jack Grealish ya yi kusan wata 12 bai ci wa Manchester City ƙwallo ba a kakar nan, bayan da yake fuskantar kalubale.

Rabon da ya ci wa City ƙwallo tun ranar 16 ga watan Disamba a gasar Premier League a wasa da Crystal Palace a Etihad.

A shekarar 2024, Grealish ya buga karawa 25 a City a dukkan fafatawa, wanda ya bayar da ƙwallo uku aka zura a raga daga ciki.

Rauni ne ya hana Grealish sakat a kakar nan, amma duk da haka ya buga wasa a City a bana na sama da minti 1,200.

City tana ta biyu a kan teburin Premier League da tazarar maki takwas tsakani da Liverpool mai jan ragama.

City za ta karɓi bakuncin Feyenoord a Champions League a Etihad ranar Talata, wadda take fatan komawa kan ganiya, sakamakon koma baya da ta ci karo.

Ƙungiyar karkashin Pep Guardiola ta yi rashin nasara biyar a jere a dukkan fafatawa, karon farko da aka doke kociyan ɗan kasar Sifaniya wasa biyar a jere a tarihi.

Ranar Asabar Tottenham ta je Etihad ta ci City 4-0 a wasan mako na 12 a Premier League, karo na uku a jere da aka doke ƙungiyar a babbar gasar tamaula ta Ingila a bana.