Arnold zai yi jinya sakamakon rauni a wasan Aston Villa

Trent Alexander-Arnold

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Likitoci sun auna koshin lafiyar Trent Alexander-Arnold sun tabbatar cewar raunin da ya ji ranar Asabar a Premier League ba mai muni bane.

Au sauya ɗan wasan kafin hutu bayan raunin da ya ji a wasan da Liverpool ta doke Aston Villa a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar.

A minti na 25 aka sauya mai tsaron bayan a karawar da Liverpool ta yi nasara da ta kai ga ci gaba da zama a kan teburin Premier da tazarar maki biyur tsakani.

Arnold zai yi jinyar mako biyu, kuma Liverpool za ta kara a Premier League da Southampton ranar 24 ga watan Disamba, wanda da kyar ya koma wasa a lokacin.

Idan Arnold bai warke ba koci, Arne Slot zai yi amfani da Conor Bradley a wasan na babbar gasar tamaula ta Ingila.

Da zarar Liverpool ta gama wasa da Southampton a Premier, za ta je Real Madrid a Champions League ranar Laraba 27 ga watan Nuwamba.

Kwana uku tsakani ta karɓi bakuncin Manchester City a Anfield a wasan mako na 12 a Premier League karawar hamayya.

Arnold ba zai buga wa Ingila Nations Legue ba da za ta fafata da Girka da kuma Jamhuriyar Ireland.