Yadda karayar tattalin arziki ke tilastawa 'yan Labanon shiga ƙungiyar IS

Ya na zaune ne a birnin Tripoli da ke arewacin kasar Labanon, ɗaya daga cikin wuraren da talauci ya fi yawa a yankunan tekun Mediterranean.
Duk da tsawon awannin da yake sa a aiki, daloli kadan ya ke samu a sati.
Yana bukatar kula da mahaifiyarsa mara lafiya, amma kudin da yake samu daga aikin leburancin da yake yi ba su wadatar da ciyar da su biyu ba.
Hakan ya sa ya fara laluben mafita dimin taimakawa mahaifiyasar.
Ya haɗu da wani mutum a wani gidan cin abinci inda ya shaida wa Ahmed cewa shi yake daukar wa kungiyar IS mayaka – masu tsattsauran ra’ayin Islama na Sunni wadanda suka kai hare-hare a Syria da Iraq inda kuma suka aikata kashe-kashe a wasu sassa daban-daban a duniya.
Ahmed ya ce "Ina karatun Shari'a (dokokin Musulunci), kuma ana koya mana jihadi a kowace rana. Sun faɗa mana game da Iraq da kungiyar IS. Muna son kungiyar IS, saboda shaharar da ta yi. Wani mutum da ke kurkuku ya tutube ni, ya ce min zan tura ka can'."
Ahmed na da nutsuwa sosai don haka bamu ganin kamar zai iya zama mayaki.
Muna Magana kan mugan ayyukan da kungiyar ta aikata, sai na tilasta masa ya gaya mana dalilin da ya sa yake son shiga kungiyar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya amsa da cewa "Ina son na shiga kungiyar IS na zama mujahid saboda ba zan iya jure wannan tashin hankalin ba."
Ahmed ya yanke shawara. Ya faɗawa mai daukan mutane aiki a kungiyar cewa yana son ya shiga kungiyar, kuma yana so ya bar Labanon don ya je ya yi yaƙi a matsayin ɗan kungiyar IS a Iraq da Syria.
Amma jim kadan bayan haka, 'yan sanda suka kama shi.
Jami'n leken asirin sojojin Labanon sun masa tambayoyi har na tsawon kwana biyar kafin suka sake shi.
Hakan ya sa ya yi nadamar zaɓin da yayi, amma har yanzu bai da mafita ga damuwarsa mai dimbin yawa.
"Ina ji kamar na kashe kaina. Mutane na bi na bashin kudi da na ranta don siyan kayan ɗaki amma ba zan iya biyansu ba. Ba mu san me zai faru nan gaba ba.”
A birnin Tripoli, mutane ba su cika yin fatan alhairi ba. Ana karancin wutan lantarki da ruwa da man fetur da magunguna da kuma aikin yi.
A shekarun baya da suka wuce, kusan matasa maza dari 'yan Labanon sun shiga kungiyar IS.
Ba wai shigan kungiyar ba ce burinsu, face gudun talaucin da ke ta karuwa a kasar.
Ga mutane dayawa, addininsu ko asalinsu na nufin ba za su taba samun hanyar arziki a rayuwarsu ba.
Wannan gwagwarmayar rayuwa ta sa matasa maza da yawa shiga yanayin kaka-ni-kayi da neman mafita.
"Babu aikin yi, babu makaranta ko hanyar karatu. Kuma wasu daga cikin wadanda suka shiga kungiyar IS sun yi nadama, kuma sun yi kokarin ji daga wurin iyalansu don dawowa gida amma ba za su iya ba."

Kungiyar IS na da karfi sosai a Gabas ta tsakiya fiye da yadda take da shi a da.
A wani lokaci ta yi iko da wani yanki na kasar da ta ayyana masu ikirarin kafa daular Musulunci a fadin Syria da Iraq.
An fatattaki akasarin kungiyar a wani kazamin yaki da aka gwabza a garin Baghouz da ke kasar Syria a shekarar 2019.
Amma sauran mutanen da ba a kashe ko daure su ba, na ci gaba da kai hare-hare a wuraren da dama.
Kuma a farkon wannan shekarar, aka fara fito da karin bayani kan 'yan Labanon da ke kutsa wa su kai hari a wadannan hare-haren.
Mohammad Sablouh lauya ne mai wakiltar iyalansu da dama. Tare muka nufi Wadi Khaled inda yawancin mutanen da suka bace ke zaune.
Wuri ne mai wahalar zama, cike yake da talauci.
Yara suna wasa kullum tare da kayan wasa na wucin gadi cikin tituna masu kura.
Rikicin na nufin yara dayawa ba za su samu damar zuwa makaranta ba.
Muhammed ya yi bayani cewa "wurin nan a rabe yake da birni, kalli yadda wurin ya lalace don talauci, babu wanda ya damu da shi. Gwamnati bata yin aikin ta kan mutanen kasar kamar yadda ya kamata. Don haka za a dauki yaran nan a shigar da su kungiyar IS."
Shekara ɗaya da ta wuce, Bakr Saif ya bace. 'Yan makonni kafin aurensa, ko da yake 'yan sanda sun kama shi na dan lokaci, bayan hakan ne ya fara gina rayuwarsa da wacce zai aura. Bai faɗa wa mahaifiyarsa cewa zai bar kasar ba da jimawa ba.
Idonta cike da hawaye, mahaifiyarsa ta faɗa min cewa "Ya gaya mun zai je wurin matar da zai aura, kuma zai dawo da yamma da ya tafi, bai dawo ba har yanzu."
Mahaifinsa ya kara da cewa; "A shafukan sada zumunta muka ji labarin, bamu dai yarda da labarin ba kawai kowa sai ya fara ihu da kuka."
Mahaifiyar ta dan dakatar da kukan sannan ta ci gaba da cewa "Yana cikin annushuwa, ya na ta shirin bikinsa. Yaro ne mai hankali, mai nutsuwa. Na san duk abin da na faɗa muku za ku ce ai 'mahaifiyarsa ce', amma kuma gaskiya ne."
Ba a yi wata ɗaya ba Ummu ta samu sakon murya. A wata muryar da aka jirkita ta kamfuta inda aka gaya mata cewa an kashe ɗanta a yayin wani yaƙi da ya yi wa kungiyar IS a Iraq.
Abin mamaki an kwatantanta shi da an 'kashe' shi ba 'mutuwar shahada' ya yi ba, na biyun na da yawa kamar harshen kungiyar IS na gaske ke amfani da shi.
Iyayen Bakr ba su yarda da sakon murayar ba, da kuma abin da gwamnatin Labanon suka fada musu kan mutuwarsa.
Sun yarda cewa bai taɓa barin kasar ba, suna ganin kamar an boye shi ne a wani waje a cikin kasar Labanon.
Mahaifin Bakr ya nuna mana cikin dakin ɗansa, daki ne mai tsafta amma kuma ba kowa a ciki.
Akwai wani cakulet daya saya don ranar aurensa na nan ajiye a dakin, ba a taba ba.

Iyayensa sun ce Bakr Saif ya bata ne mako kadan kafin aurensa
Sojojin Iraq sun ce Bakr ya bar Labanon zuwa shiga kungiyar IS.
Suna zargin cewa ya na cikin wani hari da aka kai wa sojoji a Diyala wanda ya yi sanadinkashe sojoji 10.
Bayan kwana kadan sojojin Iraq suka kai harin ramuwa kan kungiyar IS inda suka kashe mutum tara, rabin mutanen da aka kashe 'yan Labanon ne.
Sojojin Iraq sun ce Bakr na ɗaya daga cikin wadanda aka kashe.
Sun ce sun tabbatar da cewa shi dinne, sun kara da cewa sun yi gwajin kwayoyin hallitta na DNA kan duk wanda suka kashe don su tabbatar da wane ne shi.
Na yi magana da Janar din sojojin iraq, Yahya Rasoul Abdulla kan batun mazan da ke son barin Labanon zuwa kungiyar IS. Ga shawarar da ya basu.
"Shawarar da zan bai wa larabawa a duk faɗin duniya musamman 'yan Labanon ita ce wannan kungiyar IS din ya yi amfani da su ne tamkar itacen wuta. Za ku iya tambayar wadanda suka tashi karkashin mulkin IS – suna ta kashe mutane, suna yi wa mata fyaɗe, sun mayar da mata bayi, sun kuma rushe gado, hadda ma ɓata makabartar annabi. Kar ku kara musu kwarin gwiwa, kar ku yarda su yi amfani da ku.
Sojojin iraq na ko ina, duk inda wannan kungiyar za ta je, ko cikin sahara ko tsauni ko kwari, za mu bi su mu kashe su."

Janar din sojin Iraq Yahya Rasoul Abdulla ya ba da kalmomi masu karfi ga wadanda suke son barin Labonon don shiga IS
A farkon shekarar an samu masu shiga kungiyar sosai amma zuwa yanzu lambar masu shiga kungiyar ta ragu sosai.
Labarin wadanda suka shiga kungiyar ya zama abin koyi ga mutanen Tripoli.
Amma duk da ci gaban tabarbarewar tattalin arzikin Labanon da kuma ginkirin samun sabuwar gwamnati da 'yan siyasa suka yi, mutane na shan wahala.
Hakan ya sa kungiyar IS din suka ci gaba da neman masu shiga kungiyar.











