Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan wasannin Talata da Laraba
Kungiyoyi 32 ne za su ci gaba da wasa na bibiyu a rukuni na Gasar Champions League ranar Talata da kuma Laraba.
Wasa tara za a buga ranar Talata da kuma wadansu tara ranar Laraba a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai a wannan kaka.
Ana sa ran kafa tarihi a wasu wasannin, sannan wasu 'yan kwallon ka iya kafa bajinta, yayin da wasu kungiyoyin za su fara sanin inda alkiblarsu ta dosa.
Hakan ne ya sa muka zakulo muku wasu batutuwan da suka kamata ku sani a fafatawar da za a yi ranar Talata da ta Laraba a zagaye na biyu na gasar.
Wasannin Talata 3 ga watan Oktoba
- Union Berlin da Braga
- Salzburg da Real Sociedad
- Man United da Galatasaray
- Copenhagen da Bayern
- Lens da Arsenal
- PSV Eindhoven da Sevilla
- Napoli da Real Madrid
- Inter vs Benfica
Kroos zai buga wasa na 100 a Champions League
Wasan Napoli da Real Madrid shi ne zai fi jan hankalin duk wani mai bibiyar tamaula a ranar Talata. Za dai a buga wasan ne a Italiya.
Toni Kroos kuma zai buga wasa na 100 a Champions League. Dan kwallon zai zama na 27 da ya yi wannan bajintar a kungiya daya.
Har yanzu dan wasan kasar Jamus din, mai shekara 33 yana da rawar da yake takawa a kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama.
Wasannin Laraba 4 ga watan Oktoba
- Atlético Madrid da Feyenoord
- Antwerp da Shakhtar Donetsk
- Celtic da Lazio
- Dortmund da Milan
- Newcastle da Paris
- Leipzig da Man City
- Crvena zvezda vs Young Boys
- Porto da Barcelona
Ko Leipzig za ta taka wa Haaland burki?
Kungiyar Leipzig ba za ta so kara haduwa da Erling Haaland ba, ba don komai ba sai don kwallo biyar da ya zura musu a raga.
A bara ne City ta caskara kungiyar ta Jamus 7-0 a zagaye na kungiyoyi 16, inda kungiyar Ingila ta kai zagayen gaba da kwallo 8-1 gida da waje.
Haka kuma Haaland mai shekara 23 ya zura kwallo shida a ragar Leipzig lokacin da yake taka leda a Borussia Dortmund.
Jimilla Halland ya ci Leipzig kwallo 11 a wasa shida da ya fuskanci kungiyar ta Jamus.
Pepe zai sake fuskantar Barcelona
Ko za ka iya tuna sunan Cristiano Ronaldo, Lionel Messi, Sergio Ramos, Xavi Hernández da sauransu? sunayen da aka rika ambato a shekarun baya yayin wasa tsakanin Real Madrid da Barcelona.
Duk lokacin da za a buga wasan na hamayya da ake kira El Clasico abubuwa kan dauki zafi, inda har sai mahukunta sun dau tsauraran matakai.
Kenan tsohon dan wasan bayan Real Madrid, Pepe zai fuskanci Barcelona ranar Laraba, kuma a karon farko da zai fuskanci kungiyar Camp Nou tun bayan 2017.
Pepe mai shekara 40 ya fuskanci Barcelona a lokacin da yake taka leda a Sifaniya sau 23 da yin nasara 10 aka doke su 10.
Lokutan da za a buga wasannin rukuni a Champions League:
Wasa na bibiyu a cikin rukuni: 3/4 ga watan Oktoba
Wasa na uku-uku a cikin rukuni: 24/25 ga watan Oktoba
Wasa na hur-hudu a cikin rukuni: 7/8 ga watan Nuwamba
Wasa na biyar-biyar a cikin rukuni: 28/29 ga watan Nuwamba
Wasa na shida-shida a cikin rukuni: 12/13 ga watan Disamba