Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Real Madrid da aka je da su Napoli
Real Madrid ta ziyarci Napoli, domin buga wasa na biyu a cikin rukuni ranar Talata a gasar Champions League.
Real, wadda take da maki uku a rukuni na uku, ta ci Union Berling 1-0 a wasan farko cikin rukuni ranar Laraba, 20 ga watan Satumba.
Napoli ce ke jan ragamar rukunin da maki uku, bayan ta je ta yi nasara a kan Sporting Braga 2-1 a dai ranar ta Laraba 20 ga watan da ya wuce.
Real Madrid, mai Champions League 14, jimilla tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 21, bayan karawa takwas.
Ita kuwa Napoli mai maki 14 tana ta uku a kan teburin Serie A na bana, bayan kammala karawar mako na bakwai.
Napoli ba ta taba lashe Champions League ba a tarihi.
Jerin fafatawa tsakanin kungiyoyin biyu a gasar Zakarun Turai:
Champions League 2016/2017
Talata 07 ga watan Maris din 2017
- Napoli 1 - 3 Real Madrid
Laraba 15 ga watan Fabrairun 2017
- Real Madrid 3 - 1 Napoli
European Cup 1987/1988
Laraba 30 ga watan Satumbar 1987
- Napoli 1 - 1 Real Madrid
Laraba 16 ga watan Satumbar 1987
- Real Madrid 2 - 0 Napoli
'Yan wasan Real Madrid da za su kara da Napoli:
Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Cañizares.
Masu tsaron baya: Carvajal, Nacho, Lucas V., Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Carrillo.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma Ceballos.
Masu cin kwallo: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.
Wasannin da za a kara ranar Talata:
- Red Bull Salzburg da Real Sociedad
- FC Union Berlin da Sporting Braga
- Manchester United da Galatasaray
- FC Kobenhavn da Bayern Munich
- Inter Milan da Benfica
- RC Lens da Arsenal
- PSV Eindhoven da Sevilla