Watakila Antony ya buga wa Man United wasa da Galatasaray

An wallafa

Watakila Antony zai buga wa Manchester United wasan Champions League da za ta kara da Galatasaray ranar Talata.

Rabon da dan kwallon na kasar Brazil ya buga wa United tamaula, tun farkon watan Satumba, bayan an zarge shi da cin zarafin wasu mace.

Antony, wanda ya musanta dukkan zargin da ake yi masa, 'yan sanda ba su tsare shi ba a Brazil ko a Burtaniya.

Ya koma yin atisaye ranar Lahadi, dalilin haka koci Erik ten Hag ya ce watakila ya yi amfani da dan kwallon a wasa na biyu a cikin rukunin farko na gasar ta Zakarun Turai.

Ten Hag ya tabbatar da cewar likitoci za su yi wa dan kwallon baya Lisandro Martinez aiki a kafarsa da ya fama rauni.

Mai shekara 25 dan wasan tawagar Argentina bai buga wa United wasannin karshe a kakar da ta wuce ba, saboda karayar da ya samu a kafa cikin watan Afrilu.

Kenan United tana sa ran zai yi jinyar wata uku ko hudu kafin ya koma fagen daga.

Sai dai United za ta kara samun kwarin gwiwa, bayan da Sergio Reguilon ya murmure, bayan rashinsa a karawarsu da Crystal Palace ta ci United ranar Asabar a Premier League.

United tana da 'yan wasan da ke jinya da suka hada da Aaron Wan-Bissaka da Luke Shaw da kuma Tyrell Malacia.