Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba gaskiya ba ne da ake cewa zan koma Barcelona - Arteta
Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya ce ba gaskiya ba ne kan rahoton da ake yi cewa zai koma aikin horar da Barcelona.
Ranar Asabar Xavi ya sanar da cewar zai ajiye aikin kociyan kungiyar Camp Nou da zarar an kammala kakar bana.
Wasu jaridun Sifaniya sun ruwaito cewar Arteta, wanda ya fara tamaula a karamar kungiyar Barcelona, zai bar aikin jan ragamar Arsenal.
''Wa ni? ba haka ba ne. Labarin ba na gaskiya ba ne,'' in ji Arteta, wanda yake da kunshin kwantiragi da Gunners zuwa karshen kakar 2025.
''Raina a ɓace yake kan labarin da kuke karantawa. Bai da wani tushe balle makama.
''Ina wajen da ya dace da mutanen da suka kamata, kuma ina murna da hakan.
''Na rungumi alaka da nake da ita da Arsenal hannu bibbiyu, kuma muna da abubuwan da za mu cimma tare nan gaba, bayan jituwa mai kyau tare da shugabannin kungiyar.''
Arteta bai buga wani babban wasa ba a Barcelona, wanda ya je wasannin aro a Paris St Germain - ya taka leda a Rangers da Real Sociedad da Everton da kuma Arsenal.
Bayan da ya yi ritaya, ya fara aikin koci karkashin Pep Guardiola a Manchester City daga nan ya karbi aikin horar da Arsenal a Disambar 2019.
A matakinsa na kociyan Gunners ya lashe FA Cup a 2020, kuma Arsenal ta kare a mataki na biyu, bayan da Manchester City ta lashe kofin a bara.
Gunners tana mataki na uku a kan teburin bana da tazarar maki biyar tsakaninta da Liverpool, wadda ke jan ragamar teburin.
Ranar Talata, Arsenal za ta je gidan Nottingham Forest a wasan mako na 22 a gasar Premier League. Gunners ta ci wasan farko 2-1 cikin Agustan 2023.
Haka kuma Arsenal, wadda aka fitar daga FA Cup da Carabao Cup tana cikin wasannin Champions League zagaye na biyu da za ta fuskanci Porto.