An tashi baran-baran tsakanin PENGASSAN da Matatar Dangote

Motocin dakon mai a matatar Dangote

Asalin hoton, @DangoteGroup

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ƙungiyar manyan ma'aikatan kamfanonin iskar gas da fetur PENGASSAN ta ce tana nan kan bakarta na ci gaba da yajin aiki bayan kasa samun maslaha tsakaninta da matatar Dangote.

Bangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi karkashin jagorancin ministan kwadago na Najeriya Mohammed Dingyadi a ranar Litinin.

A ranar Litinin ne ƙungiyar PENGASSAN ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani saboda matakin matatar Dangote na korar wasu ma'aikatanta kimanin 800.

Babu dai wata sanarwa daga ɓangaren Matatar Dangote bayan tattaunawa da kungiyar PENGASSAN, amma a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi ta ce ta sallamar ma'aikatan ne a wani mataki na ƙoƙarin daidaita tsarin aikin matatar.

Matatar Dangote ta kuma bayyana matakin yajin aikin PENGASSAN a matsayin rashin aiki da doka da kokarin zagon kasa ga Najeriya da al'ummarta.

Yajin aikin PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harakar mai a Najeriya ciki har da babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL, tare da dakatar da ba matatar Dangote ɗanyen mai.

"Muna kan bakarmu har yanzu saboda mutanenmu da aka kora daga aiki, muna so dole a mayar da su," kamar yadda Kwamred Injiniya Dauda Adamu Aliyu shugaban ƙungiyar kwadago ta TUC bangaren PENGASSAN a jihar Adamawa ya shaida wa BBC.

"Matatar Dangote har yanzu ba nuna alamar nadama ba kan abin da suka yi, don haka mu kuma ba za mu janye matakinmu ba," in ji shi.

Kodayake kungiyar PENGASSAN ta ce akwai dama ta sake ci gaba da tattaunawa domin warware rikici tsakaninta da matatar Dangote.

"Za mu koma mu tattauna a kwamitin zartarwa kafin a dawo a sake haduwa don samu mafita," a cewar Kwamred Kwamred Injiniya Dauda Adamu Aliyu.

Wannan na zuwa a yayin da wata kotu Abuja ta bayar da umarnin hana yajin aikin ƙungiyar PENGASSAN da ɗaukar matakin hana kai wa matatar Dangote danyen mai da iskar gas.

Matatar Dangote ce ta shigar da ƙarar a gaban kotun ma'aikata a Abuja, kuma alƙalin kotun ya ce Matatar Dangote kamfani ne mai zaman kansa da ke da lasisin samarwa da raba man fetur domin buƙatun ƴan Najeriya.

Duk da umarnin kotun, ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aikin domin nuna goyon baya ga PENGASSAN.