Saura maki huɗu tsakanin Real Madrid da Barcelona a La Liga

Robert Lewandoewski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Saura maki huɗu ya rage tsakanin Real Madrid da Barcelona a teburin La Liga, bayan Robert Lewandowski ya ci Alaves.

Ranar Lahadi Barcelona ta karɓi bakuncin Alaves a wasan mako na 22 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, inda ta ci 1-0.

Wannan shi ne wasan farko da Barcelona ta buga a Fabrairu, wadda ke fatan yin karawa biyar ko kuma shida a watan.

Kawo yanzu Alaves ta kasa yin nasara a kan Barcelona a wasa 15 baya da suka kara a lik, wadda aka doke karo na 13 da canjaras biyu.

Ƙungiyar da Hansi Flick ke jan ragama tana ta ukun teburi da tazarar maki uku tsakani da Atletico Madrid da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta daya.

Ranar Asabar Real Madrid ta yi rashin nasara 1-0 a gidan Espanyol, yayin da Barcelona ta yi amfani da wannan damar ta rage tazarar makin dake tsakaninsu.

Ranar Alhamis, Barcelona za ta je gidan Valencia, domin buga Copa del Rey zagayen kwata fainals.

Daga nan kuma Sevilla za ta yi wa Barcelona masauki a gasar La Liga ranar Lahadi 9 ga watan Fabrairu.