Man United za ta kara da Forest a Carabao Cup 1 ga Fabrairu

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Nottingham Forest za su buga wasa na biyu a daf da karshe a Carabao Cup ranar 1 ga watan Fabrairu.
Ranar Laraba 25 ga watan Janairun 2023, United ta je ta doke Forest 3-0 a City Ground a fafatawar farko a League Cup..
Minti shida da fara wasa Marcus Rashford ya ci kwallo, kuma na 10 a United tun bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar a Disambar 2022.
United ta kara na biyu daf da hutu ta hannun sabon dan kwallon da ta dauka a Janairu, Wout Weghorst sannan Bruno Fernandes ya ci na uku daf da za a tashi.
United za ta karbi bakuncin wasa na biyu a Carabao Cup da Forest ranar 1 ga watan Fabrairu a Old Trafford.
Wannan shi ne karo na biyu da United ta ci Forest 3-0 a kakar nan, bayan hakan da ta yi mata ranar 27 ga watan Disamba a Premier League.
United wadda ita ce kadai a Ingila da ke buga kofi hudu a bana, wato League Cup da FA da Premier da Europa na fatan daukar wani ko wasu daga ciki.
Rabon da United ta dauki kofi tun bayan doke Ajax a Europa League a 2017.
Kungiyar Old Trafford tana ta hudu a teburin Premier League, bayan wasannin mako na 21.











