An dakatar da Bentancur saboda kalaman ɓatanci ga Son Heung-min

Rodrigo Bentancur

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An dakatar da ɗan wasan Tottenham, Rodrigo Bentancur wasa bakwai, saboda kalaman ɓatanci da ya yi wa Son Heung-min.

Bentancur, wanda kuma aka ci tarar £100,000, an bukaci ya je neman ilimin da za a tsara masa na wajibi a kansa.

Hukumar ƙwallon kafar Ingila ce ta tuhumi ɗan wasan tun cikin watan Satumba, saboda wasu kalaman da ya yi a lokacin wata hira a talabijin a Uruguay a watan Yuni.

''Rodrigo Bentacur ya musanta zargin, sai dai wani kwamiti mai zaman kansa ya samu ɗan wasan da laifin da ta kai aka dauki matakin hukunci a kansa,'' in ji FA.

Mai shekara 27 zai koma taka leda a Ingila daga ranar 26 ga watan Disamba, kenan ba zai buga karawar da Tottenham za ta yi da Manchester City da Liverpool ba.

Sauran wasan da ba zai yi ba sun haɗa da na Chelsea da sauransu da wanda Tottenham za ta yi a League Cup zagayen kwata fainals da Manchester United.

Amma zai iya buga wa Tottenham wasannin gasar zakarun Turai na Europa League da take yi a kakar nan, domin hukuncin iya wasannin da ake yi a Ingila ne.

Bentancur ya buga wa Tottenham wasa 15 a kakar nan da cin ƙwallo a karon farko a ƙungiyar a wasa da Ipswich Town ranar 11 ga watan Nuwamba.