Barcelona ta lashe wasan La Liga na shida a jere a bana

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta je ta doke Villareal 5-1 a wasan mako na shida a La Liga ta ci gaba da jan ragamar teburi da lashe dukkan wasa shida da fara kakar nan.
Kenan Barcelona ta ci gaba da buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya da kafar dama a bana, koda yake mai tsaron ragarta, Marc-Andre ter Stegen ya ji raunii.
Robert Lewandowski ne ya fara zura biyu a raga, sannan ya ɓarar da fenariti, haka shima Raphinha biyu ya zura a raga a wasan da wadda Pablo Torre ya ci.
Ter Stegen, mai shekara 32 ya ji rauni tun kan hutu, sakamakon da ya kama tamaula a sama ya faɗo a kan kafarsa ya kuma gurɗe.
An canji mai tsaron ragar aka sa Inaki Pena, wanda ya taka rawar gani a wasan da ya bai wa Barcelona maki ukun da take bukata.
Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta farko a kan teburin La Liga da maki 18 a wasa shida da fara kakar nan.
A bara da suka kara a La Liga, Barcelona ce ta fara zura biyu a raga a Estadio de la Cerámica daga baya Villareal ta farke, sannan ta kara na uku daga baya Barca ta kara ɗaya ta yi nasara 4-3.
A wasa na biyu kuwa Villareal ce ta yi nasara da cin 5-3 a gidan Barcelona ranar 27 ga watan Janairun 2024.
Shi ne karo na biyu cikin shekara uku da Barcelona ta yi rashi nasara a gida a hannun Villareal.
Ƴan wasan da koci, Hansi Flick ya je da su Villareal
Ter Stegen, Cubarsí, Balde, I. Martinez, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña, Pablo Torre, M. Casadó da kuma Pau Víctor,.
Sauran sun haɗa da Lamine Yamal, Kounde, Eric, Astralaga, H. Fort, Gerard Martín, S. Domínguez, Cuenca, Guillermo da kuma A. Fernández.









