Wasannin da suke gaban Arsenal a cikin watan Oktoba

Asalin hoton, Getty Images
Karshen makon nan babu gasar Premier League, domin za a buga wasan kasa da kasa, ko dai a Nations League a Turai ko na neman shiga gasar kofin duniya.
Haka kuma za a ci gaba da wasannin neman shiga gasar kofin Afirka da wasan sada zumunta da Fifa kan ware ranakun a irin wannan lokacin.
Arsenal wadda ta buga wasa bakwai a Premier League kawo yanzu, tana ta ukun teburi da maki 17, wadda ta ci karawa biyar da canjaras biyu.
Da zarar an kammala wasan kasa da kasa, Gunners za ta yi karawa biyu a Premier League da wasa ɗaya a Champions League da kuma a League Cup a Oktoban.
Kenan Gunners za ta ci gaba da fuskantar kalubalen kakar nan, wadda za ta je gidan Bournmouth a Premier League karawar mako na takwas.
Daga nan kuma Arsenal za ta karɓi bakuncin Shakhatar Donesk a wasa na uku a Champions League, bayan da ta ci Paris St German 2-0 a makon jiya.
Haka kuma Gunners za ta yi wasa mai zafi na hamayya a Premier League da Liverpool a Emirates a dai cikin watan Oktoban karawar mako na tara.
Wasan karshe da za ta fafata a watan nan shi ne a gasar League Cup, inda Arsenal za ta je gidan Preston.
Wasannin da ke gaban Arsenal a cikin watan Oktoba:
Premier Asabar 19 ga watan Oktoba
- Bournemouth da Arsenal
Champions League Talata 22 ga watan Oktoba
- Arsenal da Shakhtar
Premier Lahadi 27 ga watan Oktoba
- Arsenal da Liverpool
League Cup Laraba 30 ga watan Oktoba
- Preston da Arsenal










