Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta kai zagayen ƴan 16 a Copa del Rey
Real Madrid ta kai zagayen ƙungiya 16 a Copa del Rey, bayan da ta caskara Deportiva Minera 5-0 ranar Litinin.
Waɗanda suka ci mata ƙwallayen sun haɗa da Valverde da Camavinga da Arda Guler da ya zura biyu a raga da kuma Modric.
Tuni itama Barcelona ta kai zagayen gaba a Copa del Rey, sakamakon da ta doke Barbastro 4-0 ranar Asabar.
Ranar Laraba 8 ga watan nan za a raba jadawalin zagayen ƙungiyoyi 16 da za su ci gaba da fafatawa ranar 15 ga watan Janairun 2025.
Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31, sai Real Madrid da 24 da Atletico Madrid da 20 da kuma Valencia mai 10.
Wasan dake gaban Real Madrid shi ne na Spanish Super Cup zagayen daf da karshe da Real Mallorca ranar Alhamis.
Kafin nan Barcelona mai fatan lashe kofin farko a 2025, za ta fafata da Athletic Club a wasan daf da karshe a Spanish Super a Saudi Arabia.
Ranar Asabar 12 ga watan Janairu za a buga wasan karshe a Spanish Super Cup, tsakanin wadda ta yi nasara a wasan Barcelona da na Real Madrid.