Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta ɗauki kofin Carabao bayan doke Chelsea
Virgil van Dijk ya jefa ƙwallo a cikin ƙarin lokaci inda Liverpool ta kai ga lashe kofin Carabao a kakar ƙarshe na Jurgen Klopp bayan ta doke Chelsea da ci 1-0 a wasan da aka buga a filin wasan Wembley ranar Lahadi.
Liverpool ta samu nasara a gasar karo na 10 duk da cewa wasu manyan ƴan wasanta na fama da raunuka, da suka haɗa da Mohamed Salah da Darwin Nunez da Diogo Jota.
Shi ma Ryan Gravenberch ya fice daga wasan bayan wani karo da suka yi da Moises Caicedo a rabin lokaci na farko.
Hakan na nufin ƙungiyar Jurgen Klopp ta lashe kofinta ta farko cikin guda huɗu da ta ke hari a kakar wasan bana.
Wannan sakamakon na nufin kocin Chelsea Mauricio Pochettino zai cigaba da fuskantar matsin lamba sakamakon rashin ƙoƙarin da ƙungiyar ke fama da ita a kakar wasan bana.
Yanzu Chelsea ta yi rashin nasara a wasannin ƙarshe guda shida a jere, ciki har da uku da su ka kara da Liverpool.