Real Madrid da Barca na zulamar Wirtz, Zirkzee ya amince ya koma Man United,

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na dab da sayen Joshua Zirkzee, har yanzu Arsenal ba ta kara kudi kan farashin da aka sanya wa Riccardo Calafiori ba, sannan Pascal Gross na shirin komawa Borussia Dortmund.
Manchester United ta amince da yarjejeniyar sirri da dan wasan gaba na kasar Holland Joshua Zirkzee kuma suna tattaunawa da Bologna kan yadda kungiyar ta Italiya ke son biyan kudin siyan dan wasan mai shekaru 23 na fan miliyan 34. (CaughtOffside)
Chelsea na son mika dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 31, da dan kasar Italiya Cesare Casadei, mai shekara 21, ga Napoli domin su taimaka wajen rage farashin dan wasan gaban Najeriya, Victor Osimhen, mai shekara 25. (Teamtalk)
Har yanzu Arsenal ba ta kara kudi kan farashin da aka sanya na fam miliyan 42.3 kan dan wasan bayan Bologna da Italiya Riccardo Calafiori mai shekara 22 ba, kuma ana ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu. (Football Italia)
Dan wasan tsakiya na Jamus Pascal Gross ya amince da yarjejeniyar sirri da Borussia Dortmund, wadanda ke tattaunawa kan sayen dan wasan mai shekaru 33 daga Brighton a kan fam miliyan 6 zuwa £8.5. (Sky Sports Germany)
Ana alakanta Tottenham da dan wasan tsakiya na Chelsea Conor Gallagher, mai shekara 24, amma da wuya dan wasan na Ingila ya koma Spurs a wannan bazarar, duba da cewa kungiyar ta kai karshen matakin kashe kudi don siyayyar yan wasa (Football Insider)
Dan wasan Newcastle United Miguel Almiron yana tattaunawa da wakilinsa game da makomarsa, inda ake alakanta dan wasan na Paraguay mai shekaru 30 da komawa Saudi Arabiya kuma Magpies za ta iya siyar da shi. (Thronicle)
Real Madrid dai na da kwarin gwiwar cewa za ta iya doke abokiyar hamayyarta ta Spaniya Barcelona wajen siyan dan wasan Bayer Leverkusen mai shekaru 21 da haihuwa kuma dan kasar Jamus Florian Wirtz. (Sports Spanish)
Wakilin golan Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 31, ya ce Manchester United na dab da daukar shi daga Aston Villa a bazarar da ta wuce amma kocin Old Trafford Erik ten Hag ya zabi ya dauko Andre Onana na Kamaru, mai shekara 28 (ESPN)
AC Milan ta gabatar da tayin farko na dan wasan bayan Tottenham da Brazil Emerson Royal amma akwai tazara tsakanin kimar darajar dan wasan mai shekara 25 da abun da ta mika a matsayin tayi. (Sky Sports Italia)
Dan wasan gaba na kasar Sipaniya Alvaro Morata na tunanin ko zai bar Atletico Madrid ya koma AC Milan, inda dan wasan mai shekaru 31 ya ce zai ci gaba da zama a kungiyar ta Spaniya har sai ya ci wani abu da su. (Corriere dello Sport)










