Arsenal ta shiga gaban Juve a zawarcin Calafiori, Bayern na neman hana Man Utd De Ligt

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta sha kan Juventus a zawarcin ɗan bayan Bologna Riccardo Calafiori, mai shekara 22, wanda tauraruwarsa ta haska a tawagar Italiya a gasar, kofin ƙasashen Turai da ake yi, Euro 2024. (Telegraph)
Matthijs de Ligt na son tafiya Manchester United, amma kuma Bayern Munich ta yi wa ɗan bayan na Netherlands mai shekara 24 farashin yuro miliyan 50. (Sky Sports)
Newcastle na son matashin ɗan wasan gaba na Nottingham Forest na Sweden Anthony Elanga. (Teamtalk), external
Paris St-Germain ta tuntuɓi Leeds United a kan ɗan gabanta na Holland Crysencio Summerville mai shekara 22. (De Telegraaf )
Brighton na sha'awar ɗan wasan tsakiya na Feyenoord Mats Wieffer na Holland da ɗan bayan Rayo Vallecano na Romania Andrei Ratiu. (Athletic)
Manchester United ta yi yunƙurin sayen ɗan gaban Bologna Joshua Zirzkee, to amma kuma tuni AC Milan ta cimma yarjejeniyar baka ɗan wasan na tawagar Holland mai shekara 23 (Calciomercato)
Manchester City za ta ɗauki matashin ɗan wasan gaba na gefe na Brazil Savio mai shekara 20, daga wata kungiyar ta cikin rukunin ƙungiyoyin da masu City ɗin suka mallaka, Troyes. (Athletic)
Chelsea ta cimma yarjejeniya a cinikin matashin ɗan bayan Boca Juniors, Aaron Anselmino na Argentina, mai shekara 19 a kan fam miliyan 14 (Football.London)
Nice ta yi watsi da tayin da West Ham ta yi wa ɗan bayanta na Faransa, Jean-Clair Todibo, mai shekara 24, na yuro miliyan 35 (L'Equipe)
Borussia Dortmund za ta karkata ga neman sayen ɗan wasan tsakiya na Tottenham, Pierre-Emile Hojbjerg na Denmark, idan har ƙungiyar ta kasa samun ɗan wasan tsakiya na Jamus Pascal Gross, mai shekara 33, daga Brighton. (Sky Sports)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shirye Manchester United take ta saurari tayi a kan Harry Maguire a bazaran nan, inda ƙungiyoyi a Italiya suke sonshi (Talksport)
Za a yi gwajin lafiyar ɗan bayan Swansea Nathan Wood a Southampton, bayan da ƙungiyar ta yarda ta saye shi a kan fam miliyan 5 a kan tsohon ɗan wasan na tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 21. (Football Insider)
Ɗan wasan tsakiya na Aston Villa Philippe Coutinho zai bar Villa a makon nan, inda ɗan Brazil ɗin mai shekara 32 yake sha'awar komawa kungiyarsa ta tun yana yaro Vasco da Gama. (Birmingham Live)
Manchester United ba ta kawar da yuwuwar barin Marcus Rashford ya bar ƙungiyar a bazaran nan ba. (Manchester Evening News)
Burnley na shirin naɗa tsohon kociyan Fulham Scott Parker a matsayin sabon kociyanta. (Football Insider)
Wolves na sa ido a kan ɗan wasan tsakiya na Juventus Arthur Melo, kafin ta sayi ɗan Brazil ɗin mai shekara 27. (Birmingham Live)
West Ham na son sayen ɗan bayan Manchester United Aaron Wan-Bissaka, na Ingila, mai shekara 26, wanda ya rage ƙasa da wata 12 ya kammala zamansa a United. (Metro)










