Richarlison na daf da komawa Tottenham daga Everton

An wallafa

Tottenham na daf da kulla yarjejeniyar daukar Richarlison daga Everton.

Richarlison, wanda dan asalin kasar Brazil ne, ana shirin auna koshin lafiyarsa a Tottenham.

Tottenham za ta saye shi kan yuro miliyan 50, sai dai akwai wasu tanade-tanade da za a cimma, kafin kulla yarjejeniya.

A yanzu dai, Richarlison ya amince da kunshin kwantiragin da Tottenham ta gabatar masa, ana fatan kammala cinikin ranar Alhamis.

Richarlison mai shekara 25, ya je Everton daga Watford kan kudi yuro miliyon 50 a 2018.

Tun bayan nan, ya ci kwallaye 53 a wasa 152 a kungiyar, wanda shi ne kan gaba a ci wa Everton kwallaye a kakar da aka karkare.

Da kyar da gumin goshi Everton ta tsira daga barin Premier League a kakar da ta wuce, yanzu za ta ci gaba da fafatawa a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Richarlison ya fara kakar wasa da aka kammala da kafar dama, bayan bugawa kasar sa Brasil gasar Copa America da kuma wasannin Olympic, inda ya zura kwallo 10 a raga.

Daga cikin kwallayen da ya ci wa Everton, sun zo ne a wasa tara na karshen kakar da aka kammala, inda Everton ta kare a mataki na 16, wanda maki hudu ya hanada fadawa Championship.

Tottenham ta samu gurbin buga gasar zakarun Turai ta Champins League, wadda za a buga a bana, kawo yanzu kungiyar ta sayo 'yan wasa da suka hada da Ivan Perisic da mai tsaron baya Fraser Forster da dan wasan tsakiya Yves Bissouma.