Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Thomas Muller aka zaba fitatcen dan kwallon Bayern a 2021/22
Thomas Muller shi ne aka zaba a matakin dan wasan Bayern Munich da yafi taka rawar gani a kakar 2021/22 da aka karkare.
Cikin watannin da aka fafata a kakar da aka karkare ya nuna mahimmacinsa a fagen tamaula a kungiyar da kwarewar da yake da ita.
Dan wasan ya bayar da kwallo 22 aka zura a raga a dukkan fafatawa, bayan da ya ci 13 a kungiyar da ta lashe Bundesliga a bana na 10 a jere na 32 jumulla.
Muller, mai shekara 32 ya yi nasara a kan Musiala da kuma Lewandowski a jerin 'yan wasan kungiyar da suka taka rawar gani a kakar da ta wuce.
Robert Lewandowski shi ne ya lashe kyautar karo biyu baya a jere a kungiyar.
Muller ya taka rawar gani a kakar 2021/22, wanda a cikin watan Mayu ya dauki kofin Bundesliga na 11, wanda ke kan gaba a yawan daukar kofin a tarihin kungiyar.
Haka kuma ya buga wasan da Bayern ta casa VFB Stuttgart 5-0 a watan Disamba a gasar Bundesliga karawa ta 292 da ya yi kenan.
Muller ya bayar da kwallo 18 aka zura a raga a Bundesliga, shi ne kan gaba a wannan kwazon.
Haka kuma kwallo 22 da ya bayar aka zura a raga a dukkan wasannin kakar da ta wuce, shi ne kan gaba a manyan gasar Turai biyar, Kylian Mbappe ne na biyu mai 21.
Tuni dan wasan ya saka hannu kan kwantiragin da zai kare a 2024 a watan Mayu a Bayern Munich, hakan zai ba shi damar kara yin wasu bajintar.