Kalubalen da ke gaban Erik ten Hag a Man United

An wallafa

Ranar Litinin sabon kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya fara jan ragamar atisayen kungiyar, domin shirin tunkarar kakar bana.

Ranar 21 ga watan Afirilu aka sanar da daura Tem Hag a matakin kociyan United daga Ajax, domin maye gurbin Ralf Rangnick.

United wadda ta yi ta shida a gasar Premier League da aka karkare, za ta fara buga babbar gasar tamaula ta bana ranar 7 ga watan Agusta, inda za ta karbi bakuncin Brighton.  

‘Yan kwallo tara Ten Hag ya samu yin atisaye tare da su daga cikin wadanda ke buga wa United wasanni da suka hada da  De Gea da Heaton da Phil Jones da Lindelof da Martial da kuma Rashford.

Sauran sun hada da Sancho da Tuanzebe da Van de Beek da wasu matasa da suka hada da Alvaro Fernandez da Alejandro Garnacho da Zidane Iqbal da Charlie Savage da Shola Shoretire da kuma Charlie Wellens.

Wasu kalubale da Tem Hag zai fuskanta

Rashin lashe kofuna

Manchester United ce kan gaba a yawan lashe Premier League, mai 20 jumulla.

A lokacin da Sir Alex Ferguson ke jan ragamar kungiyar ta taka rawar gani a Ingila da Turai da fadin duniya, amma a yanzu zancen ya sauya.

Rabon da United ta dauki Premier League tun bayan 2013, idan kuma kofin zakarun Turai ne tun bayan wanda Jose Mourinho ya dauki Europa League a 2016/17 – yanzu shekara biyar kenan.

 

Kofunan da Sir Alex Ferguson ya dauka a Manchester United:

 

Premier League: 1992–93, 1993–94, 1995–96, 1996–97, 1998–99, 1999–2000, 2000–01, 2002–03, 2006–07, 2007–08, 2008–09, 2010–11, 2012–13

FA Cup: 1989–90, 1993–94, 1995–96, 1998–99, 2003–04

League Cup: 1991–92, 2005–06, 2008–09, 2009–10

FA Charity/Community Shield: 1990, 1993, 1994, 1996, 1997, 2003, 2007, 2008, 2010, 2011[289]

UEFA Champions League: 1998–99, 2007–08

Ya yin a biyu a Champions League a 2008–09, 2010–11

European Cup Winners' Cup: 1990–91

European Super Cup: 1991

Intercontinental Cup: 1999[289]

FIFA Club World Cup: 2008[289]

 

Salon wasa da zai dace da kungiyar

Tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a 2013, United ta kasa samun wani salo da zai yi kusan wanda take bugawa a baya.

Da United tana da zafi ta kan yi anfani da gefe da kuma ‘yan wasa biyu da suka kware a cin kwallaye.

A baya ko ka ci United, sai an tashi za kayi murna, domin komai zai iya faruwa, suna taka leda, suna takura abokiyar karawa.

Haka kuma idan ka shiga Old Trafford tamkar mayanka ka je, sai an tashi za ka fayyace sakamakon wasan, inda kungiyoyi da dama kan ji tsoron karawa a gidan United.

Yanzu dai komai ya sauya, kungiyar tana ta kokarin komawa kan ganiya, amma ba ta kamo bakin zaren ba kawo yanzu.

Tun bayan da Sir Alex ya bar aikin horar da United, kungiyar ta yi amfani da koci bakwai har da na rikon kwarya da suka hada da David Moyes da Ryan Giggs da Louis van Gaal da Jose Mourinho da Ole Gunnar Solskjaer da Michael Carrick da kuma Ralf Rangnick.

Tem Hag shi ne na takwas da zai ja ragamar United, yayin da Jose Mourinho shi ne ya taka rawar gani bayan barin Ferguson, ya dauki Kofi uku har da Europa League.

 

Ko Tem Hag zai dauki Frenkie de Jong?

United ta matsa kaimi wajen son daukar De Jong daga Barcelona tsohon dan kwallon Ajax.

Kawo yanzu ta cimma yarjejeniya, amma ba ta kai ga sa hannu kan kwantigi ba, domin ba a kammala cinikin ba.

 

 

 

United ta yi amfani da ‘yan wasa bakwai wadanda ke taka leda daga gefe da suka hada da Cristiano Ronaldo da Rashford da Sancho da Greenwood da Martial da Lingard da kuma Elanga.

Sai dai kuma kungiyar ta mance ba ta da kwararren dan wasan da ke buga tsakiya tun bayan da ta Paul Scholes da Michael Carrick.

Haka kuma a fannin masu tsaron bayanta ta kasa samun tsayayyun lamba biyar da shida, bayan da Varane ke jinya.

Haka kuma Maguire wanda ta dauka a matakin mai tsaron baya mafi tsada a duniya ya dunga yin wasu kura-kuren da aka cin kungiyar.

Ten Hag ya horar da De Jong a Ajax har suka kai karawa daf da karshe a Champions League a 2018-19

 

Ko Van de Beek zai koma kan ganiya?

Wani dan wasa da zai taka rawar gani a United shi ne Van de Beek, wanda ya lashe lik din Netherlands da wani kofin a Ajax a 2019.

Van de Beek ya taka rawar gani da duniya ta shida da kwarewar da yake da ita har ta kai ga Real Madrid ta yi zawarcinsa – amma Manchester United ta dauki dan kwallon.

 Van de Beek, ya ci kwallo 41 a Ajax da bayar da 34 aka zura a raga a karawa 175, amma a Old Trafford kamar baya kungiyar.

 

 

Ko zai samarwa da Bruno Fernandes gurbi?

United ta dauki Bruno Fernandes daga Sporting a Janairun 2020, nan da nan ya nuna kansa.

A kaka daya a United aka zabi Fernandez gwarzon dan kwallon Premier League na wata-wata har karo hudu.

Kaka daya da rabi da ya yi a Old Trafford ya yi wasa 80 da cin kwallo 40 da bayar da 25 aka zura a raga.

Ya kamata Ten Hag ya samar masa gurbin da dan kwallon zai ke bugawa ko dai dan wasa daga tsakiya ko daga gefen gaba ko kuma wanda zai ke taimakawa kungiyar ta kowanne fanni.watayawa yadda kungiyar za ta yi nasara.

 

Ko zai farfado da wasa daga gefen gaba da United ta yi a baya?

 

Manchester United tana da ‘yan wasa biyu fitattu da suka kware a buga gurbin gefen gaba da suka hada da Marcus Rashford da kuma Jadon Sancho.

‘Yan wasan biyu sun kasa taka rawar da ya kamata a kakar da aka kammala.

Sancho ya koma United daga Borussia Dortmund, sai dai bai nuna kansa ba a kakar farko, wanda ya ci kwallo biyar ya bayar da uku aka zura a raga a karawa 38.

Rashin kokarinsa ya sa Gareth Gate bai gayyace shi tawagar Ingila ba.

 

 

Ko Ten Hag zai yi amfani da maaatasan ’yan wasa?

 

Ten Hag ya yi kaurin suna wajen amfani da zakakuren 'yan wasa a duk inda ya horar da tamaula.

A kungiyar Ajax shi ne ya fito da matasan ‘yan wasa suka zama zarata da suka hada da De Ligt da De Jong da Van de Beek da Timber da Rensch da Gravenberch da Kenneth Taylor da sauransu.

Saboda haka United za ta yi farinciki idan har kociyan zai zakulo matasan da take da su kamar Alvaro Fernandez da Alejandro Garnacho da Zidane Iqbal da Charlie Savage da Shola Shoretire da kuma Charlie Wellens.

Awatan Mayu dan wasa Gernacho ya ja ragamar matasan United ‘yan kasa da shekara 18 suka lashe kofin matasan da ta kai mutun 67,492 suka kalli wasan a Old Trafford.