Arsenal ta kai zagayen gaba a Carabao cikin salo

Asalin hoton, Reuters
Matashi Ethan Nwaneri ya ci ƙwallo karon farko a Arsenal yayin da tawagar ta Mikel Arteta ta doke Bolton 5-1 domin kaiwa zagaye na huɗu a gasar Carabao Cup.
Ɗanwasan mai shekara 17 da ya fara buga wasa a wasan na daren da ya gabata, ya fara jefa ƙwallo ne bayan Raheem Sterling ya bugo masa ita.
Daga baya kuma ya karɓi ƙwallo daga wajen Rice bayan 'yan bayan Bolton sun yi sakaci kuma ya kunna kai zuwa ragar Luke Southwood, inda ya jefa ta biyun a minti na 49.
Ya ci ƙwallayen ne kuma bayan ya taimaka wajen bai wa Declan Rice ƙwallon da ya ɗaɗa ta a raga daga gefen hagu.
"Kuna iya gani da idonku cewa yana wasa ne da ƙwarin gwiwa da kuma fahimtar abin da ake buƙata a filin wasa," a cewar Arteta bayan tashi daga wasan game da matashin ɗanwasan.
Sterling ne ya ci ta huɗu a minti na 64 bayan golan Bolton ya saki ƙwallon da Saka ya buga masa, sai kuma Kai Haertz da ya kammala ta biyar ɗin bayan golan ya sake dawo da ƙwallon da Sterling ya buga.
Yanzu Arsenal za ta kara da Preston mai buga gasar Championship a filin wasa na Deepdale a zagaye na gaba.







