Diallo da De Ligt sun yi atisaye a shirin wasan United da Bilbao

Asalin hoton, Getty Images
Amad Diallo da Matthijs de Ligt sun yi atisaye kwana ɗaya tsakani da Manchester United za ta kara da Athletic Bilbao a Europa League ranar Alhamis.
Ƙungiyar da Ruben Amorim ke jan ragama na shirin zuwa Sifaniya a wasan farko zagayen daf da karshe da za su fafata a San Mames.
United na fatan kai wa zagayen karshe a wasan da za a yi ranar 21 ga watan Mayu, da duk wadda ta yi nasara tsakanin Tottenham ko Bodo/Glimt.
Kenan United ta kara samun kwarin gwiwa, sakamakon atisayen da Diallo da De Light suka yi ranar Laraba a Carrington, domin shirin zuwa Bilbao.
Rabon da Diallo ya taka leda tun cikin watan Fabrairu, sakamakon rauni, shi kuwa De Light na jinya tun daga wata ɗaya da ta wuce, wanda bai yi wa United karawa shida ba a dukkan fafatawa.
Kenan za a sa ido ko United za ta je da Diallo da De Light Sifaniya, domin fuskantar Athletic Bilbao a gasar ta zakarun Turai.
Matashin ɗan wasa Bendito Mantato da Sekou Kone da kuma Jaydan Kamason sun halarci atisaye tare da mai shekara 17, Chido Obi, wanda ba a yi masa rijistar buga Europa League ba.
Lisandro Martinez da Joshua Zirkzee, sun kammala buga wa United wasannin kakar nan, sakamakon raunin da suka ji har da Diogo Dalot.
Sai dai an yi atisayen tare da Manuel Ugarte, wanda ake sa ran zai bi Amorim a fafatawar da za a yi a san Mames ranar Alhamis.











