Ko Real Madrid za ta koma ta daya a La Liga ranar Litinin?

Vinicius Junior

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta ziyarci Rayo Vallecano, domin buga wasan mako na 13 a gasar La Liga da za su fafata ranar Litinin.

Real Madrid mai wasa 12 tana ta biyu a kan teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona mai karawa 13 da maki 34.

Rayo mai maki 18 mai wasa 12 tana ta tara a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Ranar Asabar Barcelona ta doke Almeria da ci 2-0, hakan ne ya sa ta hau kan teburin La Liga.

Ranar Litinin Real Madrid za ta san kungiyar da za ta fuskanta a wasan zagaye na biyu a Champions League da zarar an kammala raba dawalin fafatawar.

Wasan da suka kara a bara a tsakanin Rayo da Real:

2021/2022

Sifanish La Liga Asabar 26 ga watan Fabrairun 2022  

  • R. Vallecano      0 - 1       Real Madrid      

Sifanish La Liga Asabar 6 ga watan Nuwambar 2021 

  • Real Madrid       2 - 1       R. Vallecano

Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan Real Madrid da ya ziyarci Rayo da su.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni y D. Ceballos.

Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Mariano.