Real ta bayyana 'yan wasan da za su kara da Sevilla a La Liga

Asalin hoton, Reuters
Real Madrid za ta karbi bakuncin Sevilla a wasan mako na 11 a gasar La Liga da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Asabar.
Real ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 28, Barcelona ce ta biyu da tazarar maki uku tsakaninta da Real mai rike da kofin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Sevilla mai maki 10 tana ta 10 a teburin La Liga, bayan buga wasa 10.
Wasan da kungiyoyin biyu suka kara a bara:
2021/2022
Spanish La Liga Lahadi 17 ga watab Afirilun 2022
- Sevilla 2 - 3 Real Madrid
Spanish La Liga Lahadi 28 ga watan Nuwambar 2021
- Real Madrid 2 - 1 Sevilla
Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan kwallon da Real Madrid za ta karbi bakuncin Sevilla da su.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger da F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde da Tchouameni.
Masu buga tsakiya: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr. da Rodrygo.









