Yadda ƙananan ƴan kasuwa a Legas ke rufe shaguna saboda ƙarancin takardun kuɗi

.

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Masu ƙananan sana’o’i a jihar Legas, babbar cibiyar kasuwancin Najeriya na ci gaba da rufe shagunansu saboda rashin kuɗin siyan kayayyaki, yayin da kwastomominsu suka ƙaurace musu.

Da alama har yanzu mutane na ɗari-ɗari game da amfani da takardun kuɗin duk da umarnin Ƙotun ƙoli na baya-bayan nan cewa al'umma za su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi har zuwa 31 ga watan Disambar bana.

Sai dai har yanzu, gwamnatin Najeriya ba ta ce uffan ba game da umarnin na kotun ƙoli lamarin da ya jefa mutane da dama cikin halin ɗar-ɗar.

Ɗaya daga cikin masu ƙananan sana'oi a Legas, Malam Abubakar Manaja wanda yake sana'ar ɗinki a unguwar Obalende ya ce lamarin na ci gaba da tagayyara ƴan kasuwa da kuma abokan hulɗarsu.

Malam Abubakar Manaja ya shaida wa BBC cewa matsalar ƙarancin kuɗin ta sa ya shafe fiye da wata biyu ba ya sana'arsa saboda rashin kuɗin sayen kayayyakin tafiyar da sana'ar tasa.

Ya ce halin da yake ciki ya shafi iyalinsa kasancewar "bani da abin da zan ba su, suna kuka."

A cewarsa, "idan na fito da abincina, ban isa na ci ni kaɗai ba, wane sai ya zo ya damƙa, wane sai ya zo ya yaga, yunwa ta kusa kashe mutane."

Malam Abubakar Manaja ya ƙara da cewa baya ga matsalar ƙarancin takardun kuɗin, suna kuma fuskantar matsalar intanet wajen aika kuɗi - "can wanda ka turawa bai gani ba, kai da ka tura ba ka ga gani ba", in ji shi.

Ya kuma koka kan yadda hukumar da ke da alhakin kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya ta gaza wajen sauƙaƙa wa jama'a wahalhalinsu.

Telan ya ce ya jima bai riƙe takardar kuɗi ta N1,000 ko N500 ba saboda matsalar ta ƙarancin kuɗin.

Umarnin Kotun Ƙoli ba shi da tasiri...

Ɗan kasuwar ya ce umarnin da kotun ta bayar ya taimaka sai dai matakin ba shi da wani tasiri saboda tun farko da aka ba da umarnin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin, shi kansa ya sayar da takardar kudi ta N1,000 kan N400 don gudun kar ya yi asara.

"Sai da aka wayi gari ban da ko ɗaya, sai aka ce an dawo da ita, toh ina naga amfanin umarnin?'' in ji shi.

"Na sayar da kamar N36,000, N400 aka ci gaba da bani kuma ba a bani su gaba ɗaya ba, sai dai na zo na karɓi N2,000, yau na karɓi N1,000, haka aka ce min kuɗin sun ƙare har na dangana. Har yanzu ina tunanin akwai N5,300 ba a bani ba." kamar yadda Malam Abubakar Manaja ya faɗa.