Barcelona ta zaɓi Szczesny maimakon Pena a matakin tsare ragarta

Szczesny

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Barcelona, Hansi Flick ya ce ranar Talata shi da mataimakansa sun zaɓi Wojciech Szczesny a matakin mai tsare ragar ƙungiyar maimakon Inaki Pena.

Ƙungiyar ta Sifaniya ta ɗauki tsohon golan Poland, Szczesny cikin watan Oktoba, bayan da ya yi ritaya, domin maye gurbin Marc-Andre ter Stegen, wanda ya ji rauni.

Pena shi ne ya dunga tsare ragar Barcelona a zagayen farko a kakar nan, amma sai ƙungiyar ta zaɓi Szczesny, wanda ya kama karawa biyu baya.

Tuni Barcelona ta kai zagaye na biyu kai tsaye a Champions League na bana, bayan doke Benfica 5-4, inda Szczesny ya yi kuskure biyu da aka ci ƙwallo.

Koda yake Barcelona ta yi nasara a karawa biyar da tsohon mai tsaron ragar Juventus ya kama mata gola.

Ranar Laraba Barcelona da Atalanta za su buga wasan karshe a cikin rukuni a gasar ta zakarun Turai.

To sai dai za ta yi karawar ba tare da mai tsaron baya, Andreas Christensen ba, wanda zai yi jinyar mako uku kamar yadda ƙungiyar ta sanar.

Ɗan wasan tawagar Denmark na fama da jinya, wanda rabonda ya taka leda tun cikin watan Oktoban 2024.

Atalanta na fatan kammala wasannnin a cikin ƴan takwas ɗin farko, wadda take ta bakwai a kan teburin Champions League mai ƙungiya 36 a bana.