Masana kimiyya na fafutukar binciko dalilin samuwar sammai da ƙassai

Maka-makan koguna da aka gina a ƙarƙashin ƙasa a jihar South Dakota da ke Amurka.

Asalin hoton, Matthew Kapust / SURF

Bayanan hoto, Maka-makan koguna da aka gina a ƙarƙashin ƙasa a jihar South Dakota da ke Amurka wadanda suka zamo kariya daga duk wata hayaniya da ke faruwa a doron ƙasa za su zamo wurin da za a ajiye na'urorin da za su gano sauye-sauyen da aka samu a ƙananan ƙwayoyin zarra
    • Marubuci, Pallab Ghosh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Correspondent
    • Marubuci, Gwyndaf Hughes
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Videographer and Producer
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A cikin wani ɗakin bincike da ke jihar South Dakota ta ƙasar Amurka, masana kimiyya sun duƙufa wajen samo amsar ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka shige wa ɗan'adam duhu: mene ne ya sa sarari da duniyarmu suka samu?

Waɗannan masana na rige-rigen gano wannan amsa ne da wasu gungun masana kimiyya na ƙasar Japan - waɗanda suka fara irin wannan bincike shekaru da dama da suka gabata.

Ilimin da ake da shi a yanzu kan yadda sararin subhana ya samu ya gaza yin gamsasshen bayani kan yadda aka samar da duniyoyi da taurari da falaki da muke da su.

Amma yanzu tawagogin biyu na masana kimiyya na samar da wata na'ura wadda za ta tantance ƙananan abubuwan da suka gaza girman ƙwayar zarra waɗanda ake kira 'neutrino' a turance, da fatan cewa za su samo amsoshin waɗannan abubuwa da suka shige wa ɗan'adam duhu.

Yanzu tawagar biyu ƙarƙashin jagorancin Amurka na ƙoƙarin haɗa kai domin samo amsar da ake tunanin tana cikin waɗannan ƙananan ƙwayoyin zarra na Neutrino, binciken da aka yi wa laƙabi da Deep Underground Neutrino Experiment (Dune).

Taurari

Asalin hoton, NASA

Bayanan hoto, Ilimin da ɗan'adam ke da shi a yanzu ya nuna cewa bai kamata a ce an samu duniyoyi da taurari ba idan aka yi la'akari da abubuwan da suka faru kafin samuwarsu

Masana kimiyyar za su shig wasu manya-manyan kogo guda uku masu zurfin mita 1,500 a ƙarƙashin ƙasa. Idan mutum ya gani zai hangi manyan motocin haƙa kogon tamkar ƙananan motocin roba na wasan yara.

Shugaban wannan cibiyar binciken, Dr Jaret Heise ya bayyana kogon uku a matsayin "wuraren halwar bincike".

Dr Heise ya kasance cikin masu jagorantar haƙa waɗannan kogo na ƙarƙashin ƙasa tsawon kimanin shekara 10 da suka gabata.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kogunan za su kange cibiyar binciken daga duk wata hayaniya da ƙarfin lantarki da ke cikin iska da ke sahwagi a sararin duniya. A yanzu cibiyar binciken ta kai wani mataki.

Heise ya ce "mun ci alwashin gina cibiyar bincike da za ta sauya masanaiyar da muke da ita kan falaki ta hanyar amfani da wasu na'urori, waɗanda masana kimiyya fiye da 1,400 daga ƙasashe 35 za su yi amfani da su domin amsa tambayar: dalilin da ya sa aka halicce mu."

A lokacin da sarari da duniya za su samu, abubuwa biyu ne suka wanzu: wato ɓurɓushi - wanda daga gare shi ne duniyoyi da taurari da kuma duk abin da muke amfani da shi suka samu - sai kuma akasinsu, shi ma gwargwadon yawan ɓurɓushin da suka samar da duniyoyi da taurari.

A kimiyyance ya kamata waɗannan abubuwa biyu su ga bayan juna, wanda hakan zai haifar da yanayi na 'babu'. To amma abin mamaki shi ne sai ga mu mun wanzu.

Masana kimiyya na ganin cewa sirrin gane dalilin da ya sa abubuwan da suka samar da duniyoyi suka yi galaba - har ɗan'adam ya wanzu - na cikin binciken da za a yi kan ƙwayoyin zarra na neutrino da kuma kishiyarta, wato anti-neutrino.

Masanan za su riƙa haska wani haske ƙunshe da ƙwayoyin zarran daga cibiyar binciƙe da ke can cikin ƙarƙashin ƙasa a Illinois zuwa ga na'urorin da za su ɗanfara da su a jihar South Dakota, wadda ke da nisan mil 800.

Wannan bincike haɗin gwiwa ne na masana kimiyya 1,400 daga ƙasashe 30. Cikin su akwai Dr Kate Shaw daga Jami'ar Sussex a Birtaniya wadda ta shaida wa BBC cewa sakamakon da za a samu zai sauya fahimtarmu game da sammai da ƙassai da kuma ilimin ɗan'adam game da su.

Ta ce: "Abin sha'awa ne yadda a yanzu muke da fasaha da ƙirƙire-kirƙire da kuma ilimin kwamfuta da za mu yi koƙarin warware wannan ilimi da ke a duhu."

Makeken ɗakin binciken kimiyya da ke Japan ƙunshe da ƙwayaye masu launin ruwan zinare.

Asalin hoton, Kamioka/ICRR/Tokyo University

Bayanan hoto, Makeken ɗakin binciken kimiyya da ke Japan kunshe da ƙwayeye masu launin ruwan zinare

A can ɗaya ɓarin na duniya, masana kimiyya na ƙasar Japan na amfani da wasu ƙway-ƙwayan wuta masu ƙyalli na launin zinare wajen gano wannan ilimi.

Ɗakin binciken da aka tsara shi yana ɗaukar ido, tamkar wata shigifa ce ta masu ilimin kimiyya.

Masanan na Japan za su kunna na'urarsu ta haska ƙwayoyin zarra na neutrino a cikin shekara uku, shekaru bayan na Amurka sun fara aiki.

Samun ɓangarorin biyu na aiki a lokaci ɗaya na nufin cewa masana za su bankaɗo ilimummuka fiye da idan guda ɗaya ne ke aiki, amma Dr Mark Scott na Imperial College da ke Landan ya ce "zan so tawagarmu ta zama wadda za ta fara samo wannan amsa."

Yanzu dai an fara wannan rige-rige amma sai bayan shekaru ake sa ran samun amsar. Amma ya zuwa yanzu babu amsa kan tambayar da ake yi cewa mene ne ya faru kafin wanzuwar sammai da ƙassai da kuma ɗan'adam?