Gumurzun Premier tsakanin Klopp da Guardiola a Anfield

Asalin hoton, Getty images
Liverpool da Manchester City za su kara a wasan mako na 28 a gasar Premier League a Anfield ranar Lahadi.
Sun fafata a kakar nan ranar Asabar 25 ga watan Nuwambar 2023, inda suka tashi 1-1 a Etihad,
Manchester City ce ta fara cin kwallo ta hannun Erling Haaland a minti na 27 da fara karawar, daga baya Trent Alexander-Arnold ya farke saura minti 10 a tashi wasa.
Liverpool tana ta biyu a teburin Premier da maki 63, yayin da City take ta ukun teburi da maki 62.
Ranar Asabar Arsenal ta koma ta daya a kan teburi da maki 64, bayan buga karawa 28, wadda ta ci Brentford 2-1.
Erling Haaland na Man City ne kan gaba a cin kwallaye mai 18 a raga, sai Ollie Watkins na Aston Villa mai 16 da kuma Mohamed Salah na Liverpool mai 15.
Labari da ya shafi kungiyoyin:
Ana sa ran Mohamed Salah zai buga wa Liverpool karawar, yayin da ake auna koshin lafiyar Ibrahima Konate da Joe Gomez, wadanda suka ji rauni a karawa da Sparta Prague ranar Alhamis.
Manchester City na fatan Jeremy Doku da Matheus Nunes za su buga mata wasan na hamayya.
Ana sa ran Phil Foden ya murmure, wanda ya ji karamin rauni a karawa da Manchester United, amma Jack Grealish ba zai buga wasan ba.
Abin da ya kamata ku sani kan fafatawar:
Wasa daya Liverpool ta yi rashin nasara a cikin wasa 20 na baya da ta fuskanci Manchester City a Anfield ta samu cin 13 daga ciki da canjaras shida.
To sai dai wasa daya Liverpool ta ci daga takwas a baya da ta fuskanci City, shi ne 1-0 a bara.
Wasa biyu kacal bakuwa daga tsakaninsu ta yi nasara daga 30 a Premier League, ke nan wadda ta je ta kai ziyara ke nan.

Asalin hoton, PA Media
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasa 20 da Liverpool ta ci kawo yanzu ya yi kan-kan-kan da yawan na bara a gabaki dayan wasan Premier League da ta buga.
Cikin karawa tara a baya, Liverpool ta yi nasara takwas a lik, tun bayan 3-1 da Arsenal ta doke ta ranar 4 ga watan Fabrairu.
Kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ta hada maki 22 daga wasannin da ake fara zura mata kwallo a raga a bana.
Haka kuma ta ci kwallo 10 a daf da za a tashi daga wasa a kakar nan, ba wadda ta kai ta wannan bajintar.
Wadanda suka shi ga sauyin 'yan wasa a Liverpool a bana, suna da hannu a cin kwallo 22, ke nan sun zura 11 a raga sun kuma bayar da 11 aka ci.
Darwin Nunez ya ci kwallo takwas ya bayar da uku aka zura a raga a wasa 10 a dukkan fafatawa.
Mohamed Salah ya ci kwallo 11 ya kuma bayar da bakwai aka zura a raga a wasa 19 da ya fuskanci Manchester City.
Luis Diaz ya ci kwallo a kowanne wasa uku na bayan nan a Liverpool, wanda ya yi karawa 29 ba a doke kungiyarsa ba a Premier League a Anfield.
Manchester City

Asalin hoton, epa
Manchester City na fatan cin wasa na 10 a waje a jere a dukkan karawa, kuma karo na uku a karkashin Pep Guardiola.
Ba a doke City ba a fafatawa 12 baya a lik, wadda ta yi nasara 10 da canjaras biyu.
Phil Foden yana da hannu a cin kwallo 18 a lik a bana, ke nan kakar mafi kwazo da yake bugawa.
To saie dai kuma Erling Haaland ya yi wasa uku a waje a Premier League ba tare da yura kwallo ba a raga.
Ba a doke City ba a wasa 60 da Rodri ke ciki tun bayan 1-0 da Tottenham ta ci a cikin Fabrairun 2023.
Wasannin da za a buga ranar Lahadi:
- Aston Villa da Tottenham
- Brighton & Hove Albion da Nottingham Forest F
- West Ham United da Burnley
- Liverpool da Manchester City











