World Cup 2022: Fifa ta ki yarda da zanga-zangar Denmark kan Qatar

Asalin hoton, Hummel
Fifa ta yi watsi da bukatar Denmark na neman izini ga yan wasanta su sanya rigar da suke atisaye da ita da rubutun 'yancin dan adam a gasar Kofin Duniya a Qatar.
Hukumar kwallon kafa ta Denmark DBU ta nemi 'yan wasanta su sanya riga ne mai dauke da tambarin "yancin dan adam ga kowa".
Fifa ta haramta wa kasashe sanya duk wani sako mai tattare da manufar siyasa tare da neman 'yan kwallon su mayar da hankali kan kwallon kafa.
Rigimar da BDU take yi shi ne ta amince cewa sakon na siyasa ne amma hukunci ya kamata ya zama karbabbe.
"A wajena wannan riga ce da sako mai sauki kan 'yanci duniya," in ji daraktan DBU.
Fifa na da kwarin gwiwa kan abin da ta tambaya na 'yan kwallo su mayar da hankali kan kwallo - in ji Gareth Southgate kocin Ingila.
An ta sukar Qatar kan matsayarta game da auren jinsi da 'yancin dan adam da kuma yadda take tafiyar da lamuran 'yan cirani.
Denmark za su sanya rigar da ba ta da wata kwalliya a Kofin Duniya domin nuna kin amincewa da mai masaukin baki Qatar.
Fifa ce ke kula da duk wasu abubuwa da kasashe ke amfani da su ciki har da kayan sawa, wanda suke cewa kada su zama masu manufar siyasa a cikinsu ko addini ko wani kirari.










