Bidiyon jabun naira 2000 da 5000 ya bayyana a soshiyal midiya

Asalin hoton, CBN
Wani bidiyo dauke da bandiran naira 2000 da kuma 5000 sun sake bulla a shafukan soshiyal midiya, ko da yake dai an samu bullar farko na kudin ne a shekarar ta 2020.
Amma bayan da Babban Bankin Najeriya - CBN, ya bayyana cewar zai sauya wasu kudaden kasar, sai aka soma rarraba wannan bidiyon.
Babban bankin Najeriya - CBN a wani bidiyo mai tsawon dakika 30 da ya wallafa a ranar 31 ga watan Mayu ya musanta sahihancin wannan bidiyon.
Sannan ya shawarci 'yan Najeriya cewar babu gaskiya a kan batun sabobbin manyan kudin, kuma duk wanda aka kama shi da su zai fuskanci shari'a.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
A cikin bidiyon, an yi muryar wata mace na cewa wani kwastoma ne yazo ajiye kudin a banki kuma sun kai naira miliyan 17.
Najeriya dai na da kudi na takarda a matakai takwas ne kuma mafi daraja shi ne naira 1000.
Duk da gargadin da CBN ya yi, amma an ci gaba da rarraba bidiyon jabun kudin a shafukan soshiyal midiya.
Kamar wannan misalin a ranar 18 ga watan Yulin 2021.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Rarraba wannan bidiyon a shekarar 2021, ta sa shafin bin diddigi na labaran karya - Africa Check ya bayyana labarin a matsayin na karya a ranar 20 ga watan Yulin, 2021 kuma suka gano cewa wani shafi mai suna Oriental Times ne ya soma wallafa bidiyon.
Bangaren yaki da labaran karya na BBC ya yi bincike inda ya gano cewar har yanzu shafin na aiki duk da cewar rajistar Oriental Times ya kare kuma suna shirin sayar da shi.
Bidiyon dai wanda aka gano na ƙarya ne, tuni ya yaɗu a Tuwita da Tiktok da WhatsApp da kuma Facebook.
Sashen binciken gaskiya na BBC Disinformation ɗin ya bi diddigin bidiyon da a yanzun ake yaɗawa wanda wani mai suna @smartgabriel a Tiktok mai mabiya 29,000 ne ya fara yaɗa shi.
An wallafa bidiyon a Tiktok ɗin ranar Litinin 24 ga Oktoban 2022.
An kalle shi sai miliyan 1.3 aka yaɗa shi sau 15,000 tare da danna maɓallin son sa sau 29,000 kana mutum 2000 suka yi tsokaci a kai.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da TikTok suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta TikTok da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a TikTok
A ranar 26 ga Oktoban 2022, CBN ya bayyana cewa zai ƙaddamar da sabbin kuɗaɗen naira a watan Disamban 2022.
Wannan sauyi zai shafi takardun kudin naira 100 da 200 da 500 da kuma 1000 ne.
Amma a bayanin da CBN ɗin ya saki babu batun yin kuɗin naira 2000 da 5000.










