Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta dauki Arthur Melo daga Jeventus a matsayin aro
Liverpool ta dauki dan wasan tsakiyar Juventus Arthur Melo a matsayin aro zuwa karshen kaka.
Dan wasan Brazil din mai shekara 26, ya buga wa Juventus wasa 31 a kakar da ta gabata, amma bai buga ko wasa guda ba a wannan kakar.
"Ina cike da farin cikin kasancewa a Liverpool sanye da wannan riga mai cike da daukaka," Arthur ya ce.
Ya koma Anfield domin taimakawa kungiyar saboda matsalar da take fuskanta a tsakiya, yan wasanta na fama da rauni.
"Ina cikin farin ciki ina fatan yin iya kokari na wajen ganin na ba da gudunmuwata a Liverpool," Arthur ya kara da cewa.
Ya buga wa Brazil wasa 22, tare da daga kofin Copa America a 2019 alongside tare da golan Liverpool na yanzu Alisson Becker da kuma Roberto Firmino.
Liverpool da take ta shida a teburin Premier za ta buga wasanta na gaba ne ranar Asabar da abokiyar hamayyarta Everton.