Yoro da Hojlund sun shiga jerin masu jinya a United

Leny Yoro

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sabon ɗan wasan baya na Manchester United Leny Yoro zai yi jinyar watanni uku yayin da ɗan wasan gaba Rasmus Hojlund zai yi jinyar makonni shida sakamakon raunukan da suka ji a wasan share fage da Arsenal a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Majiyoyi sun tabbatar da labarin kusan da sa'a guda kafin United ta doke Real Betis na La Liga da ci 3-2 ranar alhamis a filin wasan Sanapdragon da ke San Diego.

An ga Yoro a sansanin horon United a Jami'ar California a Los Angeles (UCLA), ranar Talata sanye da takalmin kariya yana kuma amfani da sanduna.

Hakan ya haifar da fargabar cewa ɗan wasan ya ji mummunan rauni kuma hakan ya tabbata, yayin da Yoro mai shekaru 18 zai yi jinya har zuwa ƙarshen watan Oktoba.

Hakan na nufin ba zai buga wasanni tara na gasar firimiya ba, da suka haɗa da karawa da Liverpool da Tottenham da kuma Aston Villa, ba kuma zai buga wasannin farko a gasar Carabao Cup da Europa League ba.

Hojlund wanda ya zurawa United ƙwallon farko a wasanta da Arsenal a ƙarshen mako zai yi jinya har sai bayan hutun wasannin ƙasa da ƙasa na watan Satumba, wanda hakan ke nufin ba zai buga wasa da Liverpool a Old Trafford ranar 1 ga Satumba ba.

Ya rage a gani ko hakan zai sa United ta ƙara ƙaimi a ƙoƙarin da ta ke yi na sayan Jarred Branthwaite daga Everton ko Matthijs de Ligt daga Bayern Munich da ƙungiyar ta daɗe tana zawarci.