Gwamnatin Najeriya ta ce za ta dauki mataki kan BBC

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ɗauki mataki a kan kafar yaɗa labarai ta BBC kan wani bincike na musamman da sashen binciken kwaf na kafar ta yi kan ayyukan ‘yan bindiga a jihar Zamfara, da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Ministan yaɗa labaran kasar, Lai Muhammad ya yi ikirarin cewa binciken yana ƙara kambama ayyukan ƴan bindigar da suka shafe shekaru suna kashe mutane a yankin arewacin kasar.
Mista Lai Muhammad – ya ce hukumar kula da kafofin yaɗa labaran ƙasar NBC, za ta duba takunkuman da ya kamata a sanya wa BBC, duk da cewa hukumar ba ta da hurumin kula da kafafen yaɗa labarai na ƙetare.
Daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, ya faɗa wa BBC cewa za a sanar mata da takunkuman da za a sanya mata ita da kafar yaɗa labaran Daily Trust, muddin aka same su da laifin karya dokokin aikin jarida a cikin ƙasar.
A wata sanarwa, BBCn ta ce sashenta na Africa Eye na bincike ne kan abubuwa masu sarƙaƙiya da kuma jawo ce-ce-ku-ce.
Ta kuma ce labarin, abu ne da yake matuƙar jan hankalin jama'a, don haka ba ta karya dokar aikin jarida ba.
Binciken na musamman, an yayata batunsa a sassan Najeriya da dama a cikin kwanaki uku da suka gabata.
Mutane sun nuna gazawar gwamnati wajen daƙile matsalar tsaro a ƙasar, musamman ma a yankin arewa, inda ƴan bindigar ke cin karensu babu babbaka.
A watan da ya gabata gwamnan jihar Zamfara, ya umurci ƴan jihar da su mallaki bindiga domin kare kansu daga ƴan bindiga, har ma da sanya umurnin harbi kan duk wanda aka samu yana amfani da babur.
Gwamnan ya kare matakinsa inda yake cewa hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalar rashin tsaro.











