Waiwaye: Nasarar Tinubu a Kotun Ƙoli da sakin Abdulrasheed Bawa
Kamar yadda muka saba a kowane mako, a yau ma mun yi duba kan muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Asalin hoton, FADAR SHUGABAN NAJERIYA
A wannan makon ne Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.
Hukuncin na alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro, ya ce “A ƙashe, bayan warware duk wasu lamurra game da ɗaukaka ƙarar, zan iya cewa babu hujjoji masu ƙwari game da ɗaukaka ƙarar, saboda haka an yi watsi da ita,”
“Hukuncin kotu ta baya da aka zartar ranar 6 ga watan Satumba, da ya tabbatar da nasarar wanda ake ƙara na biyu a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, an tabbatar da shi.”
Wannan dai ya kawo ƙarshen duk wata turka-turka game da batun nasarar da shugaban na Najeriya ya samu, a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Hukuncin kotun koli abin takaici ne - PDP

Asalin hoton, Atiku Abubakar
Jim kadan bayan hukucin ne kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta ce hukuncin Kotun Koli a kan ƙorafin da ta shigar tare da dan takararta Atiku Abubakar, a kan nasarar zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babban abin tayar da hankali ne.
Sanarwar da sakataren yaɗa labaran PDP na kasa, Onarabul Debo Ologunagba ya fitar, babbar jam'iyyar adawar ta jaddada cewa wani abin takaici ne a ce kotun koli ta gaza ɗabbaka tanade-tanaden doka.
Jam'iyyar ta ce 'yan Najeriya har yanzu sun kasa fahimtar yadda kotun ƙoli ta lamunci manyan batutuwan yin jabun takardu da tafka karya da shaidar zir, bisa hujjar rashin cika ƙa'idojin shigar da kara.
PDP ta ce ita, da mafi yawan al'ummar Najeriya sun kaɗu kuma sun ji takaici tare da nuna damuwa a kan tunanin Kotun Kolin, wanda jam'iyyar adawar ta ce ta yi imani ya saɓa da tanade-tanaden tsarin mulkin Najeriya da kundin dokokin zaɓen ƙasar.
DSS ta saki tsohon shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa

Asalin hoton, EFCC
Hukumar tsaro ta DSS ta saki tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, bayan shafe sama da kwana ɗari a hannun hukumar.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a daren ranar Alhamis, DSS ta tabbatar da sakin tsohon jami'in na EFCC.
DSS dai ta kama Abdulrasheed Bawa ne a ranar 14 ga watan Yunin bana, kuma tun daga lokacin take tsare da shi a hedikwatarta da ke birnin Abuja.
A jiya Laraba da dare ne hukumar ta saki Bawa, wanda rahotanni ke cewa ana binciken shi da aikata ba daidai ba a aikin sa.
An dai riƙa yaɗa wani bidiyo da ke nuna shigar Abdulrasheed Bawa gida, inda iyalai da ƴan uwa ke taya shi murna da farin ciki.
Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin zaɓe a jihohi tara

Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin hukumar zaɓe a wasu jihohin ƙasar tara.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, ta ce Tinubu ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin na tsawon wa'adin shekara biyar.
Sanarwar ta ce naɗin kwamishinonin sai ya samu amincewar majalisar dattawan ƙasar, bayan tantance su.
Kalaman Rarara sun tayar da kura a Najeriya

Asalin hoton, Dauda Kahutu Rarara/Facebook
Kalaman fitaccen mawakin siyasar nan a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara na ci gaba da tayar da kura a cikin ƙasar bayan da ya fito ya soki irin salon mulkin da tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi.
Wani bidiyon mawakin da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuno shi yana cewa sai da "Buhari ya kashe ƙasar kafin miƙa ga shugaba Tinubu."
Ya ce ya yi da-nasanin gudummawa da ya bai wa tsohon shugaban ƙasar.
"Na yi da-na-sani saboda kyakkawan zaton da na yi wa Buhari na kawo gyara a Najeriya. Amma ba mu ga haka ba har ya gama mulki," in ji Rarara.
Maaƙin ya ce sai dai Buhari ya kashe kowanne fanni a ƙasar kafin ya miƙa mulki ga gwamnatin da ke kai a yanzu










