Richarlison zai yi jinya bayan raunin da ya ji a wasa da Croatia a Qatar

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Tottenham, Richarlison zai yi jinya, bayan raunin da ya ji a wasan Quarter finals da Croatia a Gasar Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.
Tottenham na fatan dan wasan zai yi jinyar makwonni ba watanni ba, amma ana jiran sakamakon gwaji, domin a fayyace girman raunin.
Richarlison, mai shekara 25, an sauya shi a minti na 84, kafin Brazil ta yi rashin nasara a bugun fenariti 4-2, bayan da suka tashi 1-1.
Dan wasan ya ci kwallo uku a Gasar Kofin Duniya a Qatar.
Shi ne na gaba-gaba da zai yi jinya a kungiyar da Antonia Conte ke jan ragama.
Tun farko wadanda ke jinya sun hada da Dejan Kulusevski da Cristian Romero da kuma Son Heung-min.
Kenan kyaftin din Ingila, Harry Kane ba zai samu hutu ba sosai, bayan da Tottenham za ta buga da Brentford a Gasar Premier League ranar 26 ga watan Disambar 2022.
Richarlison bai yi wa Tottenham wasa shida ba kafin fara Gasar Kofin Duniya, sakamakon jinya da ya yi.











