Amurka ta sanya wa 'yan Hisbah takunkumi a Iran

An wallafa

Ma’aikatar kudi ta Amurka ta sanya takunkumi a kan jami’an Hisbah na Iran saboda zargin gallaza wa mata a Iran din.

Amurka ta dora alhakin mutuwar Mahsa Amini, budurwar da mutuwarta a hannun jami’an ta janyo tarzoma a fadin kasar, a kan ‘yan Hisbar.

Amurka ta sanya takunkumin ne a kan jami’an da ke tabbatar da da’a, yayin da tarzomar da ake ta yi a sassan kasar ta Iran, kan mutuwar Mahsa Amini lokacin da take tsare a hannun ‘yan Hisbar, ke nuna ‘yar alama kawai ta kakkautawa.

‘Yan Hisbah sun kama budurwar mai shekara 22 a babban birnin kasar Tehran saboda rashin sanya hijabi, kuma ta rasu a lokacin da take hannun jami’an a tsare.

An yi zargin cewa ‘yan Hisbar sun rika dukanta a ka da kulki.

Ma’aikatar kudin ta Amurka ta sanya takunkumin ne a kan jami’an Hisbar saboda muzgunawa da cin zarafin matan kasar, da kuma take hakkin masu zanga-zanga.

Amurkar ta kuma ware wasu manyan jami’an na Hisbah bakwai da wasu jami’an tattara bayanan sirri da wasu jami’an tsaron ta sanya musu takunkumin.

Matakin na nufin an dakatar da duk wata kadara da wasu abubuwa na wadannan jami’ai, a duk wani wuri da Amurka ke da iko.

Kuma duk wani kamfani ko cibiyar kudi ta Amurka da ta yi mu’amulla da su za ta gamu da hukunci.

Da take sanar da takunkumin, Ministar kudin Janet Yellen ta ce mutuwar Mahsa Amini, wata Karin alama ce ta irin mugunta da azabtarwar da jami’an tsaro na gwamnatin Iran ke yi wa mutanensu.

Ta bayyana marigayiyar a matsayin jajirtacciyar mace.

Rahotanni sun ce zuwa yanzu mutum akalla 30 ne aka kashe a zanga-zangar ta Iran, amma kuma ana ganin yawan zai iya żarta haka sosai.

Kuma an ce hukumomi sun katse intanet. Zanga-zangar ita ce mafi muni a Iran, nan kusa.

Da yake magana a New York inda yake halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya ce ana gudanar da bincike kan mutuwar budurwar sannan ya soki zanga-zangar da cewa abu ne na neman tayar da zaune tsaye.

Shi kuwa mahaifin yarinyar ya zargi hukumomin Iran da kantara karya.