Rogers ya tsawaita ƙwantiragi a Aston Villa zuwa 2030

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Ɗan wasan Aston Villa, Morgan Rodgers ya tsawaita yarjejeniyarsa da ƙungiyar zuwa karshen kakar 2030.
Mai shekara 22 ya koma Villa daga Middlesbrough a Janairun 2024 kan ƙwantiragin £8m da karin kudin tsarabe-tsarabe na £7m.
Ya taka rawar gani da Villa ta kare a mataki na huɗu a teburin Prremier League a bara, ya kuma zama wanda Unai Emerry ke amfani da shi a sosai a ƙungiyar.
Rogers ya ci ƙwallo uku da bayar da wasu ukun aka zura a raga a karawa 15 a bana a Aston Villa.
Yana cikin waɗanda Villa ta doke Bayern Munich da Young Boys da Bologna a Champions League ta kakar bana.
Ƙwazon da yake yi tawagar Ingila ta mika masa goron gayyata, wanda ya fara buga mata tamaula a Nations League a karawa da Girka ranar Alhamis.






