Chelsea na gab da sayen De Jong, Hernandez na son dawowa United

Asalin hoton, Getty Images
A shirin da Chelsea take na dauko dan wasan tsakiya na Netherlands, Frenkie de Jong, mai shekara 25, da dan wasan gaba na Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 33, matukar Barcelona ta yanke shawarar sayar da su. (Sky Sports)
A yanzu haka dai Chelsea din na gab da cimma yarjejeniya da Barcelona kan dauko De Jong a kan kudi sama da yuro 80m (£67.6m). (Sport - in Spanish)
Kawai abin da Chelsea ke jira shi ne matsayar da De Jong zai dauka, wanda zai fi son ya tafi Stamford Bridge a maimakon Manchester United. Haka nan Chelsea din na ci gaba da tuntubar Leicester City kan dan wasanta na baya, dan asalin Farnasa, Wesley Fofana, mai shekara 21. (Times - subscription required)
Manchester United dai a nata bangaren ba ta cire ran za ta iya dauko De Jong ba, kuma tana sa ran babu ko tantama zai tafi Old Trafford da zarar ta warware batun albashinsa da Barcelona. (90min)
Dan wasan baya na Barcelona, dan asalin Sifaniya Gerard Pique, mai shekara 35, ya yi tayin yi wa kungiyar wasa a kyauta, domin taimaka mata wurin kauce ma karya dokar La Liga ta kudaden da kungiya za ta iya kashewa, da kuma ganin ta sayo sabbin ‘yan wasa. (AS - in Spanish)
Akwai yiwuwar cewa dan wasan baya na Denmark, Andreas Christensen, mai shekara 26, da dan wasan tsakiya na Ivory Coast, Franck Kessie, mai shekara 25, wadanda ba da jimawa ba suka sanya hannu kan kwantaragin yin wasa a Barcelona za su iya barin kungiyar a kyauta, matukar aka kasa yi masu rajista gabanin wasan farko na gasar La Liga da za a fara a ranar Asabar. (ESPN)
Juventus na gab da cimma yarjejeniya da Barcelona domin sayen dan wasan gaba na Netherlands, Memphis Depay, mai shekara 28. (Sport - in Spanish)
Manchester City za ta yi kokarin ganin ta sayo wani mai tsaron baya ta bangaren hagu kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa, koda kuwa dan wasan baya na Sifaniya, Sergio Gomez dan shekara 21, wanda ke wasa a Anderlecht ya je kungiyar. (Manchester Evening News)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Paris St-Germain na gab da cimma yarjejeniya da ta kai ta kudi yuro miliyan 25(£21m) da kungiyar Rennes domin sayen dan wasan gaba na Faransa, Arnaud Kalimuendo, mai shekara 20, wanda kuma Leeds United ita ma take neman shi. (L'Equipe - in French)
Kokarin Manchester United na dauko dan wasan tsakiya, Adrien Rabiot, mai shekara 27 daga Juventus kan kudi £15m ya cije bayan da aka kasa cimma yarjejeniya kan albashin da yake so a rinka biyan sa. (Gazzetta dello Sport, via Mirror)
Wanda United ke kokarin daukowa Cody Gakpo ya ce akwai yiwuwar cewa zai ci gaba da zama a kungiyarsa PSV Eindhoven, idan har kungiyar tasa ta samu nasarar shiga gasar zakarun nahiyar Turai. Nan gaba a wannan watan ne PSV Eindhoven za ta kara, gida da waje da Rangers domin samun gurbi a gasar ta Champions league ta bana. (Manchester Evening News)
Mai taimakawa wurin tafiyar da lamurran Manchester United, Darren Fletcher ya yi tattaki har Watford domin kallon dan wasan gefe Ismaila Sarr, mai shekara 24, dan asalin Senegal, a karawar da Watford din ta yi da West Brom ranar Talata. (Mail)
Shi kuwa tsohon dan wasan Manchester United, Javier Hernandez, mai shakara 34, cewa ya yi zai dawo kungiyar ya buga mata wasa a kyauta, domin taimaka mata wurin saukake karancin ‘yan wasan gaba da take fama da shi. A yanzu dai yana wasa ne a kungiyar LA Galaxy. (Sun)
Chelsea tana son ganin ta dauko dan wasan baya na Celtic, dan asalin Croatia, mai shekara 26, Josip Juranovic, wanda kuma kungiyoyin Atletico Madrid da Manchester United ke kyallara ido a kansa. (90min)
Dan wasan baya na Arsenal, dan asalin Sifaniya Pablo Mari, mai shekara 28, na gab da komawa buga wasa a Monza da ke wasa a Italiya, a matsayin aro. (Independent)
Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester United da Chelsea, Juan Mata, mai shekara 34, ya ki amincewa da tayin da MLS ta yi masa na zuwa kungiyar, yayin da dan wasan ke ci gaba da neman kungiyar da zai tafi. (Marca, via Sun)
Bayanai na cewa AC Milan ta fara tattaunawa da dan wasan Arsenal mai shekara 22, dan asalin Belgium, Sambi Lokonga, yayin da suke ci gaba da neman dan wasan tsakiya. (Football Italia)










