Za a yi karon-batta tsakanin Real da Atletico ranar Lahadi a La Liga

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta shirya karbar bakuncin Atletico Madrid, domin buga wasan mako na 23 a La Liga da za su fafata ranar Lahadi.

Wannan shi ne wasa na hudu da za su fuskanci juna a kakar 2023/2024, inda Atletico ta fara da cin Real 3-1 a La Liga ranar 24 ga watan Satumbar 2023.

Sun hadu a karo na biyu a bana a Spanish Super Cup ranar 10 ga watan Janairun 2024, inda Real ta yi nasara da cin 5-3.

Wasa na uku da suka fuskanci juna kuwa shi ne a Copa del Rey, inda Atletico ta fitar da Real da cin 4-2 ranar 18 ga watan Janairu.

Real ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 57 da tazarar maki biyu tsakaninta da Girona ta biyu, bayan buga fafatawa 22.

Atletico Madrid ce ta ukun teburi mai maki 47, iri daya da na Barcelona a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Tuni kuma Real Madrid ta bayyana ƴan wasan da za ta yi amfani da su a Santiago Bernabeu, domin fuskantar Atletico a fafatawar hamayya.

Ƴan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da kuma Diego Pineeiro.

Masu tsaron baya: Carvajal, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, D. Ceballos da kuma Arda Guler.

Masu cin kwallo: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.