Tsagaita wuta a Gaza ka iya dakatar da kashe-kashe amma ba za ta ƙarƙare rikicin ba - Sharhi

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Jeremy Bowen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Yarjejeniyar tsagaita wuta wata abar cigaba ce. Abar da aka daɗe ana jira ce.
Daftarin yarjejeniyar daban-daban na kan teburin tattaunawa tun watan Mayu na bara. Hamas da Isra'ila suna zargin juna da jan kafa.
Martanin Isra'ila ga harin da Hamas na ranar 7 ga watan Okotoban 2023 da ya janyo kisan mutum kusan 1,200 mafi yawancin ƴan Isra'ila, al'amarin da ya janyo rugurguza yankin Gaza. Mafi yawancin al'ummar yankin fiye da miliyan biyu sun yi ƙaura.
Bisa alƙaluma daga ma'aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta, Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 50,000 da suka haɗa da mayaƙa da fararen hula. Wani nazari da aka yi a mujallar the Lancet ya ce akwai yiwuwar an rage alƙaluman.
Babban ƙalubale na farko shi ne tabbatar da cewa tattaunawar ta faru. Manyan jakadun ƙasashen yammaci na fargabar cewa bayan zango na farko na yarjejeniyar da zai kwashe kwanaki 42, yaƙin ka iya yin kome.
Yaƙin na Gaza dai na da matuƙar tasiri a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wani abu dai shi ne cewa yaƙin na Gaza bai janyo yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya ba baki ɗayansa ba kamar yadda mutane da dama suka yi fargaba - Gwamnatin shugaban Amurka mai barin gado, Joe Biden na iƙrarin samun nasarar tabbatar da yarjejeniyar.
Har kawo yanzu ƙungiyar Hamas na iya yin yaƙi duk da cewa ƙarfin nata ba kamar a baya ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kotun manyan laifuka ta duniya ta zargi firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da tsohon ministansa na tsaro da aikata kisan kiyashi.
Hezbollah a Lebonan ta shiga yaƙin, daga baya kuma hare-haren Isra'ila suka gurgunta ta wani dalili daga dalilan da ya janyo kifar da gwamnatin Assad a Syria.
Iran da Isra'ila kuma sun yi musayar hare-hare - abin da ya ɗan karya lagon Iran. An kuma gurgunta ƙawayenta da ke yi mata yaƙi da take kira "Ƴan gwagwarmaya".
Ƙungiyar mayakan Houthi a Yemen sun hana da dama jiragen ruwa yin safara a tsakanin Turai da Asiya da ke bin ruwan Maliya. Yanzu dai abin da ya rage a gani shi ne ko za su cika alƙawarunsu cewa ba za su daina kai wa jiragen hare-haren ba har sai an cimma tsagaita wuta a Gaza.
Dangane kuma da yaƙin da ake tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa, wani abu ne maras daɗi da ya daɗe yana faruwa.
Saboda haka tsagaita wutar ka iya - idan aka yi dace - dakatar da kashe-kashen da kuma sakin mutanen da ake garkuwa da su daga dukkan ɓngarorin su samu su koma ga iyalansu.
Amma ba za ta kawo ƙarshen rikicin da ya kwashe fiye da ƙarni guda ana fafatawa.











